Filing Talla

Filing Talla Ga Mai Bukata Sai Ya Tuntube Mu

Zuwa Ga Matasa 2


Fatima Muhammad Ahmad✍🏼
 Kaduna Press

Ya zamu yi magana ne a kan Girman Ubangiji da kuma Tsari sa Daga wancan duniya (duniyar mahaifa) zuwa duniyar rana, haske, hankali, nufi da dogaro da kai, lallai malamai sun bude mana kofofin sanin wannan duniya ta hanyar irin bincike-binciken da suka yi ta gudanarwa, sannan kuma suka bayyanar mana da sirruka da kuma abubuwan da suka shige mana duhu na dabi'a da kuma abubuwa masu rai; irinsu dabbobi da tsirrai. Kamar yadda kuma suka bude mana kofar sanin duniyar 'yan'Adam da abubuwan mamaki na cikinta da kuma karfin fahimta, magana da kuma tunani.

Hakika karanta irin wadannan abubuwa da malamai suka binciko mana, zai sanya mu cikin tsananin mamaki, kuma za su fitar mana da girman Ubangiji Mahalicci da kuma samuwar Wanda Ya tsara wannan duniya.

Daya daga cikin wadannan malamai mai suna Karisi Maurisun ya wallafa wani littafi da ya ba shi sunan "al-Ilmu yad'u lil-Iman". A cikin wannan littafi, malamin ya yi bayani kan girman tsarin

Ubangiji ga wannan duniya, inda ya tabbatar mana cewa dukkan wani abu da yake wannan duniya yana nuni ga girman Mahaliccinsa ne, lallai mutum yakan fahimci samuwar Allah da kuma girmanSa yayin da yake karanta wannan littafi.

 Wannan marubuci yana cewa:

"Duniya takan juya sau guda a duk sa'o'i ashirin da hudu, ko kuma abin da ya yi daidai da mil dubu a ko wani awa guda. To amma a halin yanzu an kiyasta cewa tana juyawa da abin da ya yi daidai da mil dari kawai a duk sa'a guda. To amma me ya sa ba hakan ba? Don haka, a irin wancan hali, dare da ranarmu za su kasance masu tsawo fiye da yadda suke a halin yanzu har sau goma. A irin wannan hali, rana za ta kona tsirranmu a ko wace rana, sannan da daddare kuwa, dukkan tsirrai za su daskare.

Hakika rana wacce ita ce mabubbugan dukkan rayuwa, za ta kai darajar zafi da ya kai kimanin 12,000 ma'aunin faranhait, kuma kasa tana da nisa daga gare ta ta yadda za mu iya samun zafinta kamar yadda ya kamata. Wannan nisa tabbatacce ne kuma mai ban mamaki, sannan wannan canje-canje ya kan afku ne cikin miliyoyin shekaru; ta yadda rayuwa za ta ci gaba kamar yadda muka fadi. Idan darajar zafi ya karu a kasa da kimanin daraja hamsin a shekara guda, to dukkan tsirrai za su mutu tare da 'yan'Adam don zafi ko daskarewa.

Sannan kuma kasa takan kewaya rana kimanin mil goma sha takwas a ko wace dakika guda. Da a ce adadin kewayar tata zai kai misalin mil shida ko kuma mil arba'in a ko wace dakika, to da nisanmu da rana ko kusancinmu da ita zai kasance ta yadda zai hana wanzuwar irin wannan rayuwa ta mu da ita". Sannan kuma wannan babban malami ya ci gaba da ce wa: "Nisan wata daga gare mu ya kai kimanin mil 240,000. da a ce nisan wata daga gare mu mil 50,000 misali, maimakon wannan nisa da a halin yanzu yake tsakaninmu da shi, to da tsawonsa ya kai karfin da ambaliyar ruwa za ta mamaye dukkan kasar da take karkashin makwararan ruwa ta sau biyu a rana, har ya girgiza duwatsu, kuma da duniya ma ta ruguje saboda wannan bala'in".

Lallai yana da kyau ko wane daya daga cikinmu ya yi tunani yayin da yake karanta wannan hakika na ilimi, ya tambayi kansa ya ya aka yi aka sami irin wannan tsarin, kuma Wane ne Ya sana'anta hakan?

Hakika Alkur'ani mai girma ya amsa mana wannan tambaya, yayin da yake ce wa:

"bisa sana'ar Allah Wanda Ya kyautata kowane abu". (Surar Namli, 27: 88)

"Shi ne Wanda Ya halitta sammai bakwai, dabakoki a kan juna, ba za ka ga toggociya ba a cikin halittar Allah Mai rahama." (Surar Mulk, 67: 3) 

"Kuma rana tana gudana zuwa ga wani matab-baci nata. Wanda kaddarawar Mabuwayi ne, Masani. Kuma da wata, Mun kaddara masa man-ziloli, har ya koma kamar tsumajiyar murlin dabino, wadda ta tsufa. Rana ba ya kamata a gare ta, ta riski wata. Kuma dare ba ya kamata a gare shi ya zama mai tsere wa yini, kuma dukkansu a cikin sarari guda suke yin iyo". (Surar Yasin, 36: 38-40) 

To idan wannan ita ce duniyar kasa da sama, bari mu koma ga kogi da kuma abubuwan da suka kewaye mu.

Lallai wani irin kyau ne wannan duniya take da shi, duniyar da take cike da dabbobi, kifaye, lu'u-lu'u da murjani.

Hakika bincike da karatuttukan da kwararrun malami suka gudanar sun kai su ga gano abubuwan ban mamaki na wannan duniya, abubuwan da suke sanya mutum cikin tunani da mamakin girman wadannan sirrori da suke tattare da wadannan halittu na cikin ruwa.

Wannan sanannen malami (Karisi Maurisun) cikin wannan littafi nasa mai suna "al-Ilmu Yad'uw lil-Iman" ya nakalto mana wani labari dangane da kifin salmon da kuma macijin ruwa, inda yake bayyana cewa: "Bayan binciken da suka yi kan wadannan kifaye, malamai sun gano abubuwa masu ban al'ajabi kwarai. Wadannan kifaye su kan haihu a cikin kogi, amma sai su tafi su rayu na shekaru cikin teku, sannan daga baya su dawo cikin kogin da aka haife su. Kuma idan aka dauko su daga wannan kogi zuwa wani kogi na daban wanda suke hade, za su dinga iyo har sai sun koma cikin kogin da aka haife su.

Lallai sun san inda aka haife su, kuma suna da alaka da wajen, don haka suke neman wurin har sai sun koma wajen; don su rayu cikinsa".

Wannan malami ya sake kawo wata kissa mai ban mamaki dangane da rayuwar macijin ruwa.

Macijin ruwa ya kan yi hijira daga kogin da aka haife shi bayan ya girma, zuwa wani guri mai nisan gaske, inda zai je can ya rayu har ya mutu. Bayan isansu wannan guri da kuma haihuwa a wajen, 'ya'yayensu sukan sake shafe wannan tafiya mai nisan gaske su dawo inda aka haifi iyayensu, don su rayu a wajen. Ta haka ne dai wadannan halittu suke rayuwa.

Babu shakka wannan kissa ce mai ban mamaki wacce za ta bar mu cikin tsananin tunani da kuma tambayoyin da Alkur'ani mai girma ya amsa su cikin wadannan ayoyi:

"Ubangijinmu Shi ne Wanda Ya bai wa dukkan kome halittarsa, sa'an nan Ya shiryar". (Surar Daha, 20: 50) 
Lallai Allah Shi ne Wanda Ya shiryar da shi da kuma ba shi irin wannan ilimi.

Hakika wadannan lamurra suna bayyana mana ma'anar fadinSa Madaukakin Sarki cewa:"Malamai ne kawai ke tsoron Allah daga cikin bayinSa". (Surar Fadir, 35: 28) 

Hakika ba za mu taba sanin Allah Madaukakin Sarki ba sai ta ilimin nan dai da Alkur'ani mai girma ya kiraye mu da mu neme shi, kamar kuma yadda ya kiraye mu zuwa ga tunani da kuma amfani da hankali wajen sanin Allah Madaukaki, sanin halittunSa da kuma fahimtar littafinSa mai girma:

"Shin to, ba za su kula da Alkur'ani ba, ko kuwa a kan zukatansu akwai makullansu?" (Surar Muhammad, 47: 24) 

Hakika babban abin da zai kasance mana shamaki tsakaninmu da Ubangiji Tabaraka wa Ta'ala da kuma fahimtar littafinSa, shi ne jahilci, don kuwa daga lokacin da muka samu rabonmu na ilimi, kofofin sanin Allah za su budu mana, kana kuma hasken littafinSa zai haskaka zukatanmu

Post a Comment

0 Comments

Close Menu