Filing Talla

Filing Talla Ga Mai Bukata Sai Ya Tuntube Mu

Zuwa Ga Matasa 3


Fatima Muhammad Ahmad✍๐Ÿผ
 Kaduna Press

 Dubi Cikin Zatin

Dole ne in fahimtar da kaina, in san mutumci da kuma matsayina a rayuwa, lallai ni mutum ne, kuma babu shakka mutum yana da matsayi mai girman gaske cikin rayuwa, don haka yana da babban nauyi a rayuwarsa. Hakika an haife ni cikin mutumci da daukaka, lallai Allah Madaukakin Sarki ya arzurta ni da dukkan wadannan hakkoki, kamar yadda kuma Ya arzurta ni da wani yanki na wannan rayuwa ta duniya. Allah Ta'ala Yana ce wa:

"Kuma lalle ne Mun girmama 'yan'Adam, kuma Muka dauke su a cikin kasa da teku, kuma Muka arzurta su daga abubuwa masu dadi, kuma Muka fifita su a kan masu yawa daga wadanda Muka halitta, fifitawa". (Surar Isra', 17: 70)"

Sannan kuma kamar yadda aka halicce ni a kan fidira (hanya madaidaiciya), ina tsarkakakke daga dukkan sharri da mugun nufi, haka kuma aka halicci sha'auce-sha'auce da ji-a-jika tare da ni. Kana kuma na ci gaba da girma kana kuma kwakwalwata ta ci gaba da buduwa. Da wadannan ne na ci gaba da rayuwa, lallai hakki na ne in yi cikakken bayani dangane da dukkan wadannan abubuwa, sannan kuma in fahimci cewa ina da babban nauyin kulawa da kuma kiyaye wannan farar takarda ta rayuwata.

Lallai mutumci da kuma rayuwata ta gobe amana ce da take hannuna, ina da 'yancin tafiyar da ita kamar yadda nake so, sannan kuma in ja-goranci kaina duk yadda na so. 

Hakika hanyoyin rayuwa suna da yawa, akwai hanyoyin bata da kauce wa hanya, kana kuma akwai na alheri da shiriya.

Da dama daga cikin mutane sun kauce wa hanya, alhali kuwa tun ba su girma ba, wasunsu ma ba su wuce shekaru goma sha bakwai na rayuwarsu ba. Sun kasance masu zuwa kulob-kulob da kuma biyan sha'awarsu ta hanyoyin da ba su dace ba.

Lallai jahilci ko ji-ji da kai sun mamaye wadannan mutane, ko kuma sun bar borin mafarki da wahami ya hau kansu, ko kuma sun bari jin dadi da sha'awa sun ja-gorance su zuwa wuta, da kuma bata takardun ayyukansu. 

Hakika cibiyoyin binciken laifuffuka sun tabbatar da irin wadannan yanayi, ta yadda har al'umma suke kallon masu irin wadannan halaye kallo na wulakanci da cin mutumci. Da wuya ka ga wanda yake musu kallo tausayawa da kuma kokarin tsamo su daga irin wannan hali da suke ciki

 Please๐Ÿ™๐Ÿผ Share It To Youths ๐ŸŒน

Post a Comment

0 Comments

Close Menu