Filing Talla

Filing Talla Ga Mai Bukata Sai Ya Tuntube Mu

An saki mambobin Taliban 900 a Afganistan


Sakamakon yarjejeniyar da aka kulla tsakanin Amurka da Taliban, an saki mambobin kungiyar 900 da ake tsare da su a gidajen kurkukun Afganistan.

Kakakin Majalisar Shura ta Tsaro ta Kasa Jawid Faisal ya bayyana cewar a karkashin yarjejeniyar da Amurka da Taliban suka kulla, an sake sakin mambobin Taliban 900.

Faisal ya ce ya zuwa yanzu an saki mambobin Taliban da ake tsare da su a kurkuku su dubu 2, kuma ana sakin 'yan tawayen ne duba da ka'idojin shekaru da yanayin lafiyarsu da Taliban ta bayar a matsayin sharadin musayar fursunonin yaki.

Ya ce 'yan tawayen sun yi alkawarin ba za su sake shiga yaki ba inda aka dauki bayanan kowannensu.

Kakaki Faisal ya kuma bayyana cewar za a ci gaba da aiyukan sakin 'yan tawayen Taliban, kuma su ma suna jiran Taliban din ta saki fursunonin yaki da ta kama wadanda ke a hannunta.

A gefe guda kuma kakakin ofishin Taliban a Katar Suhail Shahin ya bayyana cewar za su saki wani bangare mai yawa na mutanen da suka kama suke tsare da su.

A ranar 29 ga watan Fabrairu a Doha Babban Birnin Katar, Amurka da Taliban suka sanya hannu kan yejerniniyar samar da zaman lafiya a Afganistan.

Post a Comment

0 Comments

Close Menu