Ana ci gaba da samun nasarar yaki da annobar Corona (Covid-19) a Turkiyya inda a kowacce rana adadin wadanda cutar ke kashewa yake raguwa.

A ranar Larabar nan mutane 30 sun sake rasa rayukansu wanda ya kawo jimillar adadin wadanda cutar ta kashe a Turkiyya zuwa dubu 4,461.

A dai wannan lokaci an yi wa mutane dubu 33,559 gwaji inda aka samu dubu 1,182 dauke da Corona.

An kuma sallami karin mutane dubu 1,576 wanda ya kawo adadin wadanda aka sallama zuwa dubu 124,369.