Filing Talla

Filing Talla Ga Mai Bukata Sai Ya Tuntube Mu

Ayyana Daren Lailatul Kadri


Lalle Alkur'ani mai girma bai ayyana wani dare ne na Lailatul Kadrin ba, in dai ban da cewa dai ana samun daren ne a watan Ramalana mai albarka. Abin da kawai ya yi bayani da kuma ayyana wannan dare shi ne hadisi da ruwayoyi:

An ruwaito daga Hassan bn Abu Ali yana cewa: Na tambayi Imam Abu Abdullah (a.s) kan "lailatul kadri", sai ya ce: "Ku nema shi cikin daren 19, 21 da 23".
Kusan dukkan ruwayoyin Ahlulbait (a.s) sun tafi a kan cewa ana samun wannan dare dai a kowace shekara, kuma a kan same shi cikin watan Ramalana, kuma yana cikin daya daga cikin wadannan darare guda uku ne muka ambata a sama. A saboda haka ne ma shi'a suke kiran wadannan darare uku a matsayin "Dararen Lailatul Kadri".

Daga Zurara ya ce: 'Na tambayi Imam Bakir (a.s) kan lailatul kadri, sai yace min: "Yana cikin darare biyu, daren 21 da 23". Sai na ce masa, ka gaya min wanne ne a cikinsu, sai ya ce: "Kai dai ka yi aiki a cikinsu biyun, daya daga cikinsu dai shi ne "lailatul kadri".

To abin da dai za mu iya fahimta shi ne cewa daren dai yana cikin daya daga cikin wadannan darare ne.

Haka nan kuma ba a ayyana lokacin da ake samun wannan dare ba a cikin dararen, don a ba wa mutum daman ci gaba da ibada dukkan daren, don kara samun lada da kuma neman gafarar Ubangiji.

Post a Comment

0 Comments

Close Menu