Fatima Muhammad Ahmad✍️
Kaduna Press

Natija da kuma nasarar sulhun Hudaibiyyah da aka yi tsakanin Manzon Allah (s) kafiran Kuraishawan Makka a shekara ta 6 bayan hijira, ta ci gaba da amfanin musulmi, inda Kabilar Khuza'a shigo cikin musulmi, ita kuma kabilar Kinanata ta koma cikin rundunar Kuraishawa, ta yadda aka samu bangarori biyu cikin wannan lokaci na sulhu da zaman lafiya.

Haka dai Allah Madaukakin Sarki ya so, nasara ta dinga samun musulmi, sannan kuma lokacin da Allah Ya so wata gagarumar nasarar ta sami musulmi, sai rikici ya barke tsakanin wadannan kabilu biyu, a lokacin da Bani Kananatan ta kai hari wa kabilar Khuza'a. Sai Kuraishawa suka goyi bayan kabilar Kananatan, to amma daga baya sai Abu Sufyan (wanda shi ne shugaban kafiran Makkan) ya fara jin tsoron wannan matsaya da suka dauka. Don haka sai ya nufi wajen Manzon Allah (s) don ya yi magana da shi da kuma neman ba da uzuri amma dai Manzon Allah (S) bai ba shi fuska ba saboda karya alkawarin da suka yi, ganin haka sai ya sake kokarin kama kafan wasu sahabbai ko dai zai sami fuska a wajen Manzon Allah (s), amma duk da hakan dai lamurra suka ci tura. Don haka sai ya koma garin Makka cikin kunya da kaskanci.

Bayan haka, saboda wannan karya alkawari da Kuraishawan suka yi, sai Manzon Allah ya fara hada runduna da nufi tafiya Makka da nufin yakan kafirai, inda ya tara runduna mai yawan gaske suka nufi Makkan. Wata ruwayan ta ce Manzon (s) ya fita ne da rundunar tasa a ranar 2 ga watan Ramalana shekara ta 10 bayan hijira zuwa Makkan, yana mai tsara al'amurran don kada yakin ya faru a cikin garin Makka saboda Haramin Allah ne.

Koda kafirai suka ga wannan runduna ta Manzon Allah (s) sai suka tsorata, Abu Sufyan ya mika wuya, ya karbi kalmar shahada saboda tsoron da dimautuwan da yake ciki. Don haka sai Manzon Allah (s) ya umurci Abbas bn Abdul Mutallib da ya tsaya tare da Abu Sufyan a inda Rundunar Ubangiji (Sojojin Musulmi) suke wucewa don ya girman Musulunci da idanuwansa. Lokacin da Abu Sufyan ya ga rundunar musulmi tana wucewa sai ya ce: "Lalle dan dan'uwankan nan (wato Manzon Allah) ya zama babban sarki". Nan take sai Abbas ya amsa masa da cewa: "Kaiconka! Ai wannan annabci kenan".

Ta haka ne Manzon Allah (s) ya sami wannan babban nasara, ya shiga garin Makka yana mai daukaka da kuma samun nasara ba tare da yaki ko zubar da jini ba. Yana mai kaskantar da kai ga Ubangijinsa, mai neman gafara da kuma godiya ga Ubangijinsa.

Idan taimakon Allah ya zo da cin nasara "Kuma ka ga mutane suna shiga addinin Allah, kungiya-kungiya"

To ka yi tasbihi game da gode wa Ubangijinka, kuma ka neme Shi gafara, lallai shi (Ubangijinka) Ya kasance Mai karbar tuba ne.
- Alkur'ani (110:1-3)

Please 🙏Share It to others🌹,