Filing Talla

Filing Talla Ga Mai Bukata Sai Ya Tuntube Mu

Daren Da Aka Sari Imam Ali (a.s) da Takobi Mai Guba 19 Ga Watan Ramadan

Fatima Muhammad Ahmad✍️
Kaduna Press

Bayan yarjejeniyar yaudara da aka yi a yakin Siffin abin da ake kira Tahkim tsakanin Amr bn Aas da Abu Musa al-Ash'ari, wasu kungiya daga cikin musulmi sun fandare wa Amirul Muminina (a.s) wanda ake kiransu Khawarij,duk da cewa Amirul Muminin din ya yi kokarin nusantar da su kan wannan tafarki da suka dauka da kuma ba su lokaci ko sa tuba amma dai sun ki yin haka, sai ma dai suka dinga tara sojoji don yakansa da kuma halalta jininsa, abin da ya haifar da yaki a tsakaninsu, yakin da ake kira da Yakin Nahrawan.

To bayan wannan yaki da kuma nasarar da dakarun gaskiya karkashin jagorancin Aliyu bn Abi Talib suka samu akan Khawarijawan,sai wasu daga cikinsu suka yi taro a Makka, suka tsayar cewa za su kashe Amirul Muminina (a.s), Mu'awiyyah bn Abi Sufyan da kuma Amr bn al-Aas, wadanda a ganinsu su ne suka hana ruwa gudu a duniyar musulmi.

Don haka sai suka tsayar cewa Abdurrahman bn Muljam (La'anar Allah Ta Tabbata a gare shi) shi ne zai kashe Amirul Muminina (a.s). Don haka sai ya fara shiri ya nufi Kufa, inda helkwatar Amirul Muminina take don aikata wannan danyen aiki nasa. Kuma ya tsara zai sari Amirul Muminin din ne a ya yin da yake salla.

Don haka tun a daren wannan rana ta 19 ga watan Ramalana shekara ta 40 bayan hijira sai ya nufi masallacin Kufa yana mai dakon isowar Amirul Muminina don ba da sallar asubahi.

To daman tun da jimawa Amirul Muminina (a.s) ya bayyana shahadar tasa a wannan rana, don daman Manzon Allah (s) ya masa bayanin hakan, don haka a wannan ranar ma da zai fita sallar asubahi sai ya ce wa 'ya'yayensa (Imam Hasan da Husaini) da su zauna a gida, kada su biyo shi masallaci kamar yadda suka saba. An ruwaito cewa lokacin da ya shirya zai fita hatta dabbobin da suke gidan sai da suka ta kuka, koda masu aikin gidan suka yi kokarin hana su, sai Amirul Muminina ya ce su barsu ba komai suke yi ba face suna juyayin mutuwarsa ne.

Koda ya isa masallaci ya kira salla, kana kuma ya fara jagorancin mutane a sallar, sai wannan la'anannen Allah (Abdurrahman bn Muljam) wanda da man ya samu wuri a sahun gaba sai ya taso ya sari Amirul Muminina a kansa, sara mai tsanani da takobinsa mai tsananin guba a jiki. Nan take Amirul Muminina ya fadi cikin jini, kamar yadda da man Manzon Allah (s) ya gaya masa wata cewa: "Ya Ali! An nuna min yadda wannan gemu naka zai jika da jinin kanka".

Allahu Akbar! Allahu Akbar!! Allahu Akbar!!!, kalmar farko da ta fara fita a bakin Amirul Muminina (a.s) ita ce Fuztu wa Rabbil Ka'aba", wallahi na sami babban rabo.

Nan take dai sahabban Amirul Muminin suka kame wannan la'anannen Allah, yayin da yake kokarin gudu bayan ya aikata wannan danyen aiki, a ka kawo shi gaban Amirul Muminin. Koda ya ga irin tsananin daurin da aka yi wa Abdurrahman din, sai ya bukaci da a sassauta masa kuma a yi masa mu'amala mai kyau. Ganin irin wannan dabi'a ta kwarai, sai ya (Abdurrahman bn Muljam) ya fara kuka, sai Amirul Muminin ya ce masa "Ai lokaci ya kure maka na tuba, don ka riga da ka aikata abin da ka aikata.".

Daga nan sai Amirul Muminin ya ba da umurnin cewa kada a kuntata wa wannan makashi nasa, kada a azabtar da shi, kada a lalata gawarsa bayan kashe shi, kada a kuntata wa iyalansa saboda wannan aiki da ya yi, haka nan kuma kada a ce za a kwace dukiyansa. Allahu Akbar! adalcin Amirul Muminina ba wai kawai ya tsaya ga masoyansa ba ne hatta ma ga makiyansa.

Bayan haka sai aka dauki Amirul Muminina (a.s) aka kai shi gida, inda ya ci gaba da rayuwa cikin wannan tsanani na ciwo har lokacin da Allah Ya karbi ransa yana a matsayin shahidi. Kafin hakan kuwa ya ci gaba da amsa tambayoyi da kuma yin wasiyoyi daban-daban ga mabiyansa da kuma 'ya'yansa.

Post a Comment

0 Comments

Close Menu