Filing Talla

Filing Talla Ga Mai Bukata Sai Ya Tuntube Mu

Daren (Lailatul) Kadri 19, 21, 23 Ramadan


Hakika Mu Muka saukar da shi (Alkur'ani) a cikin dare mai alkadari (lailatul kadri), To me ya sanar da kai abin da ake cewa Lailatul Kadri. 

Lailatul Kadri ya fi watanni dubu, Mala'iku da Ruhu (Mala'ika Jibril) suna sauka a cikinsa da izinin Ubangijinsu saboda kowane umurni, Sallama ne shi daren, har fitar alfijir.
- Alkur'ani (97:1-5)

A wannan dare ta "Lailatul Kadri" ne Allah Madaukakin Sarki Ya sauka da dukkan Alkur'ani mai girma gaba dayansa daga "Lauhil Mahfuz" zuwa ga Manzon Allah (s). 

Allah Madaukakin Sarki Yana fadi cikin Alkur'ani cewa: "Hakika Mu Muka saukar da shi a cikin dare mai albarka" wannan dare kuwa shi ne Daren "Lailatul Kadri". 
To sai dai kuma daga baya Mala'ika Jibril (a.s) ya kan kawo wa Manzon Allah (s) ayoyin Alkur'anin a hankali a hankali har cikin shekaru 23.

To amma kuma yana da kyau a fahimci cewa ba wai farkon saukan ayoyin Alkur'ani a daren lailatul kadri ba ne, ko kuma wai an saukar da wasu ayoyin Alkur'anin a daren lailatul Kadri ba ne, don kuwa idan har haka ne, to wace falala wannan dare ya ke da shi kenan a kan sauran darare, tun da dai ai an saukar da wasu ayoyin ma a wasu dararen? Haka nan kuma ba wai an saukar da surar "Inna Anzalnahu" ba ce a wannan dare, saboda fadin Allah Madaukakin Sarki cewa: "Hakika Mu Mun saukar da shi", don lamirin "shi" din yana komawa ne ga Alkur'ani ba wai ga ita kanta surar ko kuma wata aya ta cikinta ba ne.

Don haka saukar da Alkur'ani gaba dayansa ne aka yi shi a wannan dare mai albarka - daga "Lauhul Mahfuz" zuwa ga zuciyar Manzon Allah (s), kana daga baya kuma aka dinga sauko da ayoyin kadan-kadan, gwargwadon abin da ya faru a lokacin.

Post a Comment

0 Comments

Close Menu