An samo daga Abu Abdullah (a.s) yana cewa: "Duk wanda ya karanta surar "Inna An zal nahu" cikin sallarsa ta farilla, wani mai kira zai ce "Ya bawan Allah, an gafarta maka zunuban da ka yi".

An ruwaito Imam Bakir (a.s) yana cewa: "Duk wanda ya karanta surar 'Inna An zal Nahu', kuma ya bayyana muryarsa, kamar wanda ya fitar da takobinsa ne fi sabilillah (jihadi), wanda kuma ya karanta ta a boye da yawa, Allah Zai share masa zunubai dubu daga cikin zunubansa(6)".

Falalar Lailatul Kadri:

An so a yi wanka a wannan dare, ibada, addu'a, Ziyarar Imam Husain (a.s) da dai sauransu har zuwa fitowar alfijir. To daga cikin falalolin wannan dare kuwa, har da:
Duk wanda ya tsaya (ibadu) a daren lailatul kadri, yana mai imani da neman lada, Allah Zai gafarta masa zunubansa da ya aikata.
Lallai shaidan ya kan buya cikin wannan dare, ba zai fito ba har sai bayan fitowar alfijir din wannan dare.

Albarkoki da ni'imomin Allah su kan sauka a wannan dare, haka nan kuma Ya kan kare mutum daga dukkan sharrorin da wani ya nufe shi da su.

Da dai sauransu. Ana iya komawa ga littattafan da suka yi bayani a kan wannan dare. 👇👇
____________
(1)- Surar Dukhan; 44:3.
(2)- Surar Dukhan; 44:4-6.
(3)- Al-Mizan fi Tafsiril Kur'an: 20/333.
(4)- Majma'ul Bayan: 9-10/787.
(5)- Majma'ul Bayan: 9-10/784.
(6)- Tafsirul Safi; 5:353.