A yau 22/5/2020 ne Yan Uwa HARISAWA (maza) almajiran Sayyid Ibrahim Zakzaky na yankin Kaduna sun gudanar da daga tutar Falastinu kamar yadda a ka gudanar a sassa daban daban na Duniya.
Ranar Duniya ta Qudus, Rana ce ta raya tahiri tare da karya lagon Isra'ila wacce Imam Khumaini (k.s) ya asassa, ya sanya a ranar Juma'a ta karshen ko wani watan Ramadan ya zama ranar tunawa da Wahalhadu da Zalluncin da Al'ummar 
Palastinawa ke sha a hannun yahudawa sahyoniya. Amm bisa yana yin da muka tsinci kanmu a cikin na wannan Annobar Coronavirus (COVID-19), sai ya kasance lamarin ya saba da yadda a ka saba yi duk Shekara, na muzaharori a manyan titina na buranen Kasashen duniya.
Hakika wadan nan yan manayar (yan daban) yahudawa, sun mamaye  tin daga tekun Meditrenia har zuwa gadar tekun Jodan suka mamaye kuma su ka kwace daga Ahlinsa na asali, lokaci ba zai sanya a amince da HKI ba, hanya guda daya tilo ya rage wa Al'ummar Falastinu da masu goyon bayan Al'ummar Palastinu ita ce hanyar gwagwarmaya. Zamu cigaba da gwagwarmayan da nu na goyan baba ga Al'ummar Falastinu.
A karshe muna kira da kasashen yankin da suka amince da halarcin Isra'ila, bayan amincewa da wannan haramcecciyar kasa, sun hada kai da ita wajen yakar kungiyoyin gwagwarmaya.
irin ta'addancin da HKI tare da hadin kan masarautar Ali sa'oud ke yi a kasashen musulmi, da kisan gillan da Sojojin Najeriya suka yi a ranar 12/12/2015 ga almajirai Shekh Ibrahim Elzakzaky sama da dubu (1,000+) a garin Zaria tare da hadin guwar kasashen Amurka, Isra'ila gami da masarautar Ali-sa'oud, ta kar kashin kasa. Tabbas wannan lamari ne da tarihi ba zai manta da shi ba. 
Rawar da kasar Amurka da HKI ke takawa a kasashe kamar su Siriya, Yemen, Bahren gami da Libiya ya hana a samu mafuta sai dai kara rura wutar yaki suke yi, halartar 'yan ta'adda a taron na ba-bayan nan na Herzliya a HKI shike tabbatar cewa magaban tel-Aviv na da hanu dumu-dumu wajen yakin kasar Siriya da Yemen sauran karshe she.

Zamu ciga ba da wannan gwagwarmayan don samun yanci, da neman uzuri a wajen Ubagiji, muna kara kira da babban murya ga gwamnatin kasar nan da ta gaggauta sakar mana jagoran mu ba tare da wani sharadi ba. A karshe muna kara fadin #FreeZakzaky #FreePalestine.

Hurras Kaduna Unit
22/5/2020