Filing Talla

Filing Talla Ga Mai Bukata Sai Ya Tuntube Mu

IRAN Ba zamu zama sanadin barkewar yaki a Gabas ta Tsakiya ba - Iran
Wasu 'yan kasar Iran a birnin Teheran, yayin ziyarar bajakolin sabbin makamai masu linzami da kasar ta kera.
Wasu 'yan kasar Iran a birnin Teheran, yayin ziyarar bajakolin sabbin makamai masu linzami da kasar ta kera.

Rundunar sojin Iran tace ba za ta zama sanadin barkewar yaki a yankin Gabas ta Tsakiya ba, duk da cewa a ‘yan watannin da suka gabata dangataka tayi tsami matuka tsakaninta da Amurka, babban bayan kashe kwamandanta Qassem Soleimani da Amurkan tayi a Bagadaza, babban birnin kasar Iraqi.Alwashin na Iran ya zo ne kwanaki kalilan bayan harba tauraron dan Adam na ayyukan soja da tayi zuwa sararin samaniya, da kuma barazanar mayar da kakkausan martani muddin sojin ruwan Amurka suka kaiwa jiragen ruwanta hari.

Wata sanarwa da sojin na Iran suka fitar, ta nuna cewar ba za su taba takalar fada ko kuma haddasa rikicin da zai shafi yankin Gabas ta Tsakiya ba, sai dai za su cigaba da kare kansu a duk lokacin da aka takale su.

Rundunar tace duk wata tsokana da barazana  daga kowacce kasa, musamman Amurka zai gamu da martanin da ya dace.

IRANPost a Comment

0 Comments

Close Menu