Filing Talla

Filing Talla Ga Mai Bukata Sai Ya Tuntube Mu

SHIN WAI DA GASKE NE AN BAWASU TAKARDAN SHIGA ALJANNA TIN A NAN DUNIYA?

>==>Isiya Sy✍️
Kaduna Press
isiyasym@gmail.com

Tafarkin da Shi’a suka bi wurin bayar da matsayi ga sahabbai wadanda su ne musulmi na farko shi ne gaskiya, domin shi ne abin da musulunci ya zo da shi. 

Musulunci bai ware wasu musulmi ba ya ba su garanti na duk abin da suka ga dama su yi, sannan kuma ya ware wasu ya takura su da cewa idan suka yi laifi zasu tafi wuta. 

Mai daraja Imam Bakir (a.s) yana cewa:" babu wani kusanci na jini tsakanin wani da Allah, mafi soyuwar bayi wurin Allah, kuma mafi darajarsu gunsa, su ne mafi takawarsu mafi aikinsu da biyayyarsa

Ya Jabir ba a kusanta zuwa ga Allah sai da biyayya, kuma ba mu da amintuwa daga wuta, kuma ba mu da wata hujja a kan Allah. 

Duk wani mai bin Allah shi ne masoyinmu, kuma duk wani mai sabon Allah shi ne makiyinmu, wallahi ba a samun soyayyarmu sai da aiki. 

(Alwasa'il: babi 63, daga babin hukuncin tufafi, H; 5). 

Don haka ne ma Al Qur'ni ya ba mu misalai da matar Annabi Nuhu (a.s) da matar Annabi Ludu, da dan Annabi Nuhu (a.s), da Abulahab ammin manzon Allah (s.a.w), duk zamansu tare ko kasancewarsu na jinin wadannan bayin Allah bai amfanar da su daga kare su daga azaba ba yayin da suka saba ko suka canja. 

Sunna da suka nemi ganin dukkan sahabbai adalai ne alhalin sun kawo wadannan hadisai, ga kuma ayoyin Kur’ani suna karyata wannan magana tasu, ba mu san yadda zasu iya samar da mafita ga alakakan da suka fada ba. 

Yaya zasu fassara kisan da A’isha da Dalha da Zubair da sauran sahabbai suka yi wa Usman? Sannan kuma yaya zasu yi da kafirta Usman da A’isha ta yi, wacce fatawarta tana cikin dalilan kashe shi? Yaya zasu fassara yakar Imam Ali (a.s) da wadannan sahabbai suka yi, da kuma abin da Mu'awiya ya yi na yakarsa ? 

Da sauran dubunnan tambayoyi da ba su da iyaka. 

Mu sani musulunci ya sanya ma'auni ga tsira shi ne imani na gari, da ayyuka na gari, da mutuwa a kai. 

Allah ba shi da alaka ta jini da kowa koda kuwa Annabi (s.a.w) ne, hatta da Annabi (s.a.w) da zai yiwu ya canja da Allah ya azabtar da shi balle sauran mutane.

Post a Comment

0 Comments

Close Menu