Filing Talla

Filing Talla Ga Mai Bukata Sai Ya Tuntube Mu

Jihar Kogi Na Fuskantar Matsin Lamba Saboda Rashin Cutar Coronavirus Ko Daya Sabunta wa ta karshe Mayu 13, 2020


Jihar kogi da ke Arewa ta tsakiyar Najeriya na ci gaba da zama gagara badau akan rashin samun cutar coronavirus da ta zama ruwan dare game duniya.

Hukumomin jihar sunyi korafin cewa ana tursasa masu domin su bayyana samun cutar coronavirus a jihar, kamar yadda Kwamishinan Lafiya na jihar Dr. Saka Haruna ya bayyana.

Shi ma Kwamishinan Labarai na jihar Kingsley Panwo, ya tabbatar da cewa suna shan matsin Lamba akan wannan al’amari cewa, inda ta kai har ana zargin gwamnatin jihar da boye wa duniya ko da akwai cutar a jihar.

Ya ce, babu wani abu da suka boye, abinda suke zato ko fata daga cibiyar kula da cututtuka masu yaduwa wato NCDC shine, ta taimakawa jihar domin ci gaba da kare al’ummarta daga kamuwa ko yaduwar wannan cuta.

Wani mazaunin Lokoja, babban Birnin jihar, Dr.Umar Lokoja ya ce, idan har an sami bullar cutar coronavirus a jihar to babu abinda za a iya boyewa.

A makwabciyar jihar Naija kuwa, Gwamnatin jihar ta kara wani wa’adin makwanni biyu na dokar hana fita domin dakile yaduwar cutar coronavirus, kamar yadda Gwamnan jihar Alh. Abubakar Sani Bello ya Bayyana.

Acikin makwanni biyun, gwamnatin ta ware ranakun Talata, Jumma’a da Kuma Lahadi domin Jama’a su dan sarara na wasu ‘yan Sa’o’i, sai dai gwamnatin jihar ta haramta Sana’ar kabu-kabu ko Achaba Kwata-kwata a cikin makwanni biyun.

Safuwan Sp harun
Kaduna press

Post a Comment

0 Comments

Close Menu