Kasar Turkiyya ta taimakawa yara 60 'ya'yan marasa karfi da suturan lokuttan sanyi a kasar Paraguay.

Kamar yadda ofishin jakadancin Turkiyya dake Asuncion ta sanar Hukumar Hadin Kai da Taimako ta Turkiyya (TİKA) ta taimakawa yara 60 'ya'yan talakawa da kayayyaki iri daban daban da suka hada da suturar lokacin sanyi.

Jakadan Turkiyya a Asuncion, Armağan İnci Ersoy, ya sanar da cewa a garin Caaguazu sun taimakwa yara da dama kayayyakin sanyawa a cibiyar Nemity mai nisan kilomita 180 daga babban birnin kasar Asuncion.

Ersoy, ya kara da cewa sun kuma taimakawa yaran da kayan abinci.