A ranar 12 ga watan ramadan tun farkon isowar Manzon Allah (s) garin Madina bayan hijira, abin da ya fara shi ne gina masallaci, inda zai kasance fadar gwamnatin Musulunci kana kuma wajen tattauna mas'alolin Musulunci da kuma musulmi, bugu da kari kuma kan ibadun da ake yi a wajen. Baya ga haka kuma sai ya fara kokarin gina wata al'umma ta musulma, ma'abuciya hadin kai da kuma taimakekeniya a tsakani.

Don cimma wannan buri ne na gina al'umma musulmi ma'abuciya hadin kai da fahimta juna bugu da kari kan taimakekkeniya tsakanninsu, ya sa Manzon Allah a ranar sha biyu ga watan Ramalana, shekara ta farko bayan hijira, ya hada 'yan uwantaka tsakanin Muhajirai (mutanen Makka) da Ansarawa (Mutanen Makka). An ruwaito cewa a wannan rana, Manzon Allah ya hada Abubakar da Kharija bn Zaid a matsayin 'yan uwa, kana kuma Umar da Utban bn Malik, tsakanin Muaz bn Jabal da Abu Zar Gaffari, Ammar bn yasir da Hazaifa bn Yaman, Mus'ab bn Umair da Abu Ayyub Ansari, sannan Salman kuma da Abu Darda'i.

Haka nan Manzon Allah (s) ya hada 'yan uwantaka tsakanin dukkan musulmi, Muhajirai da Ansar in banda Imam Ali (a.s). Don haka sai Imam Ali (a.s) ya zo wajen Manzon Allah (s) yana kuka, cikin sai ya ce masa:Ya Rasulallah! Na ga ka hada 'yan uwantaka tsakanin sahabbanka, amma ni ba ka hada ni da kowa ba? sai Manzon Allah (s) ya ce masa: "Kai dan'uwana ne a duniya da lahira.

To ta haka ne Manzon Allah (s) ya hada sahabbansa, kuma aka sami fahimtar juna tsakanin musulmi a wancan lokaci, lamarin da ya sanya Ansarawa sukan saki matansu don Muhajiri ya samu ya aura, sannan kuma suke fifita 'yan'uwansu a kan kansu.

Babu shakka kuwa wannan 'yan uwantaka da Manzon Allah (s) ya hada tsakanin Sahabbansa ya sa an samu gagaruman nasara da kuma ci gabantar da musulunci