Rufai@govkadunaCopyright: @govkadunaLikitoci a jihar Kaduna ta Najeriya sun yi watsi da hujjojin da gwamnatin jihar ta bayar na rage wa ma’aikatan jihar albashi da kashi 25%.
A farkon makon nan ne gwamnatin ta sanar da yin ragin albashin ga ma’aikatan da ke daukar albashin da ya haura naira dubu 67 zuwa sama domin samun abin da za a tallafa wa masu karamin karfi.
Dr. Emmanual Joseph shugaban kungiyar likitocin ta kasa reshen Kaduna ya ce hgar an fara yankar albashinsu na watan Afrilu.
"Sun fara (yankar albashi) ba su yi mana magana ba," in ji shi. "Maimakon gwamnati ta yaba mana kan aikin da muke yi sai ta zo da dorina ta yi mana duka."
Ya ci gaba da cewa: "Babbar kungiyarmu ta kasa ta rubuta musu cewa ba mu yarda da wannan magana ba. Muna jiran martanin gwamnatin tukunna kafin mu dauki mataki na gaba."
Article share tools  Kaduna press