An sanya wa wannan daren suna "Lailatul Kadri" ne don shi ne daren da Allah Madaukakin Sarki Ya ke kaddara abubuwa, Yake kaddara abubuwan da za su faru cikin shekara, na daga: rayuwa da mutuwa, alheri da sharri, arziki, haihuwa da dai sauransu. Muna iya tabbatar da hakan kuwa ta fadin Allah Madaukakin Sarki cewa: "A cikinsa ne ake rarraba duk wani al'amari mai hikima, Al'amari ne daga wurinmu, hakika Mu Mun (kasance) Masu aikowa ne, Wata rahama ce daga Ubangijinka, hakika Shi Shi ne Mai ji Masani".

Don haka "raba al'amari mai hikima" yana nufin kaddara al'amurra da dukkan abubuwan da suka kumsa da kuma tabbatar da su a wannan dare mai albarka daga Allah Madaukakin Sarki zuwa ga bayinSa.

Sannan kuma akan ce al-Kadr: da ma'anar matsayi, a kan ce masa (wato daren) "lailatul kadr" saboda muhimmanci da kuma matsayinsa, da kuma girman masu ibada a cikinsa. Don raya wannan dare da ibada da ayyuka na kwarai irin su salla, zakka da dai sauran ayyukan alheri, sun fi ayyukan da mutum zai yi cikin watanni dubu da babu "lailatul kadri" a cikinsu.