Az~Zahra Badamasi Ishaq✍️
Kaduna Press

Fada da yakin da masu daure wa haramtacciyar kasar Isra’ila gindi da kawayensu wadanda su ma masu goyon bayan Isra’ilan ne amma ba a hukumance ba suke yi da ranar kudus, yaki ne abin kallo. Sun samar wa ranar kudus kishiya sannan kuma suna ta kokarinsu wajen ganin an mance da wannan ranar.

Mu dai ba mu taba ganin wani waje a duniyar musulmi da masu karfi na duniya suka ba da dama ga gwamnatocin kasashen wajen su bude fage wa mutane su gudanar da jerin gwanon ranar kudus ba.

Abin bakin cikin shi ne cewa siyasar masu karfi na duniya sun sami kutsawa da fadi a ji cikin da dama daga cikin kasashen musulmi Hakan kuwa yana daga cikin matsalolin da kasashen musulmin suke fuskanta.

Wani dalili ne ya sa gwamnatocin kasashen musulmi ba za su kwadaitar da al’ummominsu fitowa wajen jerin gwanon ranar kudus ba ?

Shin wani abu ne zai ragu daga cikin abubuwan da suke da su? Idan har sun yi imani da kuma yarda da mas’alar Palastinu, to me ya sa ba sa bada izinin (jama’a su fito don gudanar da jerin gwanon ranar kudus din ba) ?

Ya kamata Kowannen Mu Yayi Tinanin Wannan Lamari!!

Please Share It to others🌹