Fatima Muhammad Ahmad✍️
Kaduna Press

Babu wani bambanci tsakanin mazhabobin Musulunci sannan kuma dukkanin (malaman) fikihun (mazhabobin Musulunci) sun tafi kan cewa matukar dai makiya suka kwace wani yanki daga cikin yankunan musulmi sannan kuma suka tabbatar da ikonsu a wannan yankin, to wajibi ne dukkanin al’ummar musulmi su yi dukkanin abin da za su iya wajen dawo da wannan yanki zuwa ga ikon musulmi.

Don haka wajibi ne dukkanin al’ummar musulmi a duk inda suke a duniya su ji cewa wannan wani nauyi ne da ke wuyansu.

Ko da yake da dama ba za su iya yin wani abu ba; to amma duk wani mutumin da zai iya yin wani abu, ta kowace hanya ce kuwa zai iya yin din, to wajibi ne ya yi wani abu kuma ma suna yin hakan.

A saboda haka ne dukkanin duniyar musulmi suka yi na’am da sanarwa da marigayi Imam Khumaini (r.a) ya yi na sanya kowace juma’ar karshen na watan Ramalana a matsayin ranar kudus ta duniya.

Ranar kudus dai ba ta ta’allaka da kasar Iran ko Najigerya kawai ba; rana ce ta Musulmin duniyar.

A saboda haka a dukkanin duniyar musulmi, al’ummar musulmi suke bayyanar da kasantuwarsu a fili don nuna goyon baya da kuma ba da kariyarsu ga ‘yan’uwansu Palastinawa.

A wannan ranar, al’ummar musulmi suna tabbatar da iradar da suke da ita ce wajen fuskantar albarusan Amurka da haramtacciyar kasar Isra’ila a kasar Palastinu da ake zalunta