Filing Talla

Filing Talla Ga Mai Bukata Sai Ya Tuntube Mu

Ranar Qudus Ya Sake Zagayowa


Wajibi ne mu gudanar da (Bukukuwan) Ranar Kudus, qudus ta duniya, domin sake jaddadawa da kuma tunatar da musulmin duniya masu kishi nauyin da yake (wuyansu) wajen ba da kariya da kuma goyon bayan al’ummar Palastinu da ake zalunta sama da shekaru 70.

Imam Khumaini (r.a), ya sanar da irin wannan rana (ta qudus ta duniya) don sake tabbatar da kuma farkar da Al'ummar duniya batun Palastinu a cikin samuwa da zukatan bil’adama sannan kuma ya taro dukkanin tofin Allah tsinen (da ake yi) da kuma jefa su a kan yahudawan sahyoniya.

A kowace shekara kuwa muna ganin irin yadda al’ummar musulmi suke yin gagarumar maraba da wannan kira da kuma kasantuwa cikin wadannan bukukuwa (na ranar qudus ta duniya). Alhamdulillah bana ma Al'umma sun ansa kira duk da bana lamarin ya canza salo, Sakamakon halin da duniya ke ciki na Annobar Coronavirus (COVID-19).

Wadannan mutane da suke cikin yankunan (Palastinu) da aka mamaye sannan kuma cikin rauni da hali na zalunta (da suke fuskanta) suke gwagwarmaya sannan kuma suke fuskantar wahalhalu wanda babban fatan kawai da ake da ita wajen ‘yantar da Palastinu da kawar da gwamnatin zalunci da ‘yan fashi (yahudawan sahyoniya) a da ta ta’allaka ne da wannan gwagwarmaya ta cikin gida wajibi ne su ji sani su san cewa a dukkanin fadin duniyar musulmi, zukatan al’ummomi cike suke da tunanin (irin halin da suke ciki) kuma za mu ci gaba da goyon baya su, da basu kariya.

Matukar dai muna son wadannan ‘yan gwagwarmaya wadanda suke tamkar baki a cikin gidajensu, su ji cewa (lalle muna tare da su), to wajibi ne mu cigaba da gudanar da irin wadannan zanga-zangogi da jerin gwano na al’umma a dukkanin fadin duniyar musulmi. Da kafafen sadarwa.

Saboda wannan ma’ana ce Imamin mu mai girma kuma babban Jagoranmu mai girma (Imam Khumaini yardar Allah ya kara tabbata a gare shi) ya kirkiro wannan rana ta kudus; idan kuwa ba haka ba to ai a fili ya ke cewa mutanen da suke fitowa kan titunan biranen nigeria da sauran Kasha she duniya (a matsayin misali), ba za su iya yaki da makamai da (haramtacciyar kasar) Isra’ila daga nan ba. Amma zamu fito mu bayyana wa duniya, kin jinin (yan fashi, yan daba, yahudawa shahayoniya) da kuma goyan bayan Al'ummar Palestine.

A Karshe muna kira ga gwamnatin NAJERIYA da ta gaggauta sakin jagoran Harka Musulunci Sheikh Zakzaky ba tare da wani sharadi ba. Muna kuma Allah wadai da haramcaciyar kasar Izira'ila (Israel). Da Amurka (America).

#FreePalestine #FreeZakzaky We Demand Justice.
_______________
15/5/2020
- Isiya Sy✍️
Kaduna Press

Post a Comment

0 Comments

Close Menu