LABARIN MUKHTAR DA 
GWAGWARMAYANSA A RAYUWA  KASHI NA (2)
✒️✒️✒️✒️✒️✒️
Bashir Kaduna✍️ 
Kaduna press

In mai karatu na biye damu a rubutu da ya gaba muntsaya ne Dai dai inda MUKHTAR yatsandara ihu bayan fitowansa gida, shi da yayan sa halima.

Mahaifiyansa tana zuwa ta dauki yaranta ta rungumai tana sharemai kasa a kansa.
Sakamakon bugashi da kasa da halima tayi da gangan sai dayayi sanadiyyan fashewan gefen goshin MUKHTAR 
Allah sarki tabon da bazai taba bacewa ba kenan har abada.

Baban MUKHTAR kuwa yafara kamuwa da wani rashin lafiya a dan wanan lokacin Wanda jiki yaki dadi sai da takai an kwantar dashi a babban asibiti a birnin katsina.

Alhaji Ahmad magajin gari Yayi fama da jinya sosai mai tsawan gaske. Sai da takai kowa yana tausayin sa, sanan gashi da yara kananan sanan Ga matsala na cikin gida, da shi kansa yasan dasu.
Yan uwan Alhaji Ahmad sunyi iyakan kokarinsu har sunfara gajiya, kullun inkazo Asibitin zakaga Mahaifiyar Ahmad Aisha ce ita daya take jinyan Alhaji duk da yanada sauran wasu Matan har biyu bayan ita.

Amma itadai alamarin mijinta yafi tsaya mata a rai. Akwana atashi jikin Alhaji Ahmad yayi tsanani takaima yafara barin wasiyya a gaban abokansa da wasu yan uwansa.

Wanan abokin nasakuwa baiyi kasa a gwiwaba yasha tambayan Alhaji ko zaka taimaka kabani MUKHTAR amana a hanuna Alhaji.?

Alhaji Ahmad yace yayana nabarsu a hanun Allah ne, Ban barwa kowa ba.
Allahu Akbar, Dama Allah yace duk Wanda ya jibanta lamarinsa gareni lallai zantaimaka masa.

Inna lillahi wa ina ilaiyin rajiun. Bayan wasu kwanaki Allah yayima Alhaji Ahmad rasuwa  yarasu yabar mata uku da yaya goma sha bakwai. Daga cikin yaransa akwai  babba a cikinsu Wanda da ita da hadin kan mamata uwar gida suka shige dakin Alhaji bayan mutuwan sa suka dibai wasu kudinshi masu tarin yawa, a tunaninsu kada ace za azo rabo na yan dakin su MUKHTAR yafi nasu yawa sabo da MUKHTAR yana da kaso biyu akan Nasu.

Allah sarki duniya kenan bayan gama takaba na matan Alhaji Ahmad. alkali da tawagansa da mai unguwa da wakilin hakimi suka hadu Dan raban gadan yayan Alhaji Ahmad magajin gari bayan tambaya da akayima abokansa da yan uwasan na ko akwai mai binsa bashi kowa yace babu.
Sanan alkali yadukufa wajan fara rabo.
Bayan kammala rabo MUKHTAR  ya tsira da gida daya da motan hawa na babanshi.
Sauran yan uwan MUKHTAR abin yayi musu zafi duk da cewa shi MUKHTAR yaro ne baima San mai ake ciki Kanin baban MUKHTAR Alhaji Abdullahi Dan kolli 
Shine yatsa kai da fata a gaban alkali dole sai anhan nantamai dukiyan MUKHTAR a hanunsa kafin yagirma ya zama yayi hankali sai yabashi. Maman MUKHTAR kuwa Aisha batace komi ba tace Allah yakaimu yakuma baka ikon rike amana..

Dan sanin hallin da dukiyan MUKHTAR take ciki dakuma wani halli xasu shiga bayan rasuwan mahaifinsu Ku biyoni rubutu na gaba 

Wanda ni Bashir Kaduna Zan kawo muku.