Jama'ah masu kallon mu muna muka
barkanmu da wannan lokaci, na ganin karshen watan Azumi lafiya. Muna rokon Allah Ya amshi ibadojinmu, Ya sake nufa mu ga wasu watannin Azumin na badin badada. ’Yan uwana yan gwagwarmayan da dukkan al’umma, Barka Da Sallah!

Zan mu yi an fani da wannan dama mu isar da wani dan takaicen sako a yayin da muke bukukuwa da rugundumin Sallah, kada mu mance darussan da muka kowa cikin Azumi. Mu siffatu da abin da muka koya da dukkan darussan cikin watan da ya gabata na Ramadan mu’amalolinmu da ayyukanmu na rayuwar yau da kullum.

A lokacin Azumi, mun koyi hakuri da juriya, don haka sai mu ci gaba da nuna wadannan muhimman halaye a kowace mu’amalarmu. Idan aiki muke yi ko sana’a, mu kasance masu hakuri da abokan aikinmu ko sana’armu. Mu kasance masu juriya da mayar da hankali ga dukkan abin da muke yi, na ibada da sauran su  Ta haka ne za mu samu nasarar rayuwa.

A lokacin Azumin da ya gabata, mun koyi kyautata mu’amala, mun nuna kauna da son juna da zumunci. A wannan karon ma, sai mu ci gaba da haka. Kada mu yanke zumunci, mu ci gaba da jaddada shi. Mu riki juna da kauna da soyayya.

Miji da mata, saurayi da budurwa, aboki da aboki, kawa da kawa, makwabci da makwabci, mu zauna lafiya, mu dauki darussan Azumi na jaddada salama da aminci tsakanin juna. Mu kauce wa husuma da tashin hankali da juna. Mu tanadi halaye da matakan kyautata wa juna da tattalin juna, yadda za mu kasance cikin amincin juna da zaman lafiya.