-Aminu Badiko
Kaduna Press

Kamar ko wace Shekara, wannan Shekarar ma Allah ya kara ara mana rayuwa, munkai wannan lokaci na tunawa da raunanan da ake Zalunta A Palestinu wanda haramtartar Kasar lsraeela ke cigaba dayi ba badare ba rana, wannan motsi na shelantawa duniya irin zaluncin da akewa raunana palastinawa ne, tasa Ayatullah  lmam Khumaini (QS) ya fitar da fatawar fitowa ga duk wanda Mutumtaka ta dameshi kuma yake girmama hankalinsa, yafito a Jumu'ar karshen ramadana domin nuna goyan baya ga palastinawa, da nuna kyama ga haramtacciyar Kasar lsraeel. 
Bisa ga yanayi da muka tsinci kanmu a fadin Duniya na wannan Annoba Covid 19, tasa aka canza salon gabatar da Shelar dan kaucewa jefa rayuka zuwa ga kamuwa da ita wannan cuta, tare da Shawarar Malamai da Masanan kiwon lafiya, hakan ta sabbaba fito da sabon tsarin yadda shelar zata gudana duk Duniya a wannan Shekarar. 
Dalilin hakane "Yan'uwa Musulmi na yankin Kaduna karkashin Jagorancin SHEIKH #Zakzaky (H) ya sabbaba sukabi sahun takwarorin su na duniya wanjen bin wannan tsarin domin Shelar tasu, Shelar ta hada da tsuraru a Jam'i da dai daiku da suka hadu a wurare mabanbanta domin isar da sakon nasu. 

Cikin wadanda suka samu damar shiga jerin mashelantar akwai; SHEIKH Aliyu Tirmizi Wakilin "Yan'uwa na garin Kaduna, wanda cikin Jawabansa metsawo akan Munasabar Ranar Qudus da dalilin ita Munasabar,  daga karshe ya karkare da bada sako ga dukkan Al'ummar Duniya, musamman Al'ummar Wannan Kasar tamu, akan cewa; yana daga wajibinsu su dubi irin Zaluncin da akema SHEIKH #Zakzaky (H) a wannan Kasa,  kuma wajibi ne suzo sutemake shi, domin awannan yanayin kana iya gane zaluncin da akewa Palestinawa ne da irin zaluncin da akewa #Zakzaky (H), domin #Zakzaky da Mabiyansa sune palastinawan wannan Kasar, agefe guda kuma Mahukuntar wannan Kasa sune Israelar wannan Kasa, Sabida haka temakon #Zakzaky (H), Tamkar temakon raunanan duniyane irinsu Palastinawan! Da sauran su.

 Daga karshe Shehin Malamin yayi nasiha ga "Yan'uwa bisa cigaba da Jajircewa wajen temakon Wannan Mukhlisin Bawa, tare da kara zage damtse wajen ribatar sauran kwanukan da suka rage a Watan. 

Zamuci gaba da kawo maku Jawaban Shehin Malamin daga yau zuwa Jumu'ar Karshen ramadana.  IA

-Aminu Badiko.