DARE NA (12).

Sallah raka'a (8) kowace raka'a Fatiha (1) Inna-Anzalnahu (30) Allah zai bai wa wanda ya yi wannan Sallah ladar masu godiya ga Ni'imarsa.

DARE NA (13).

Ana son yin Sadaka a daren. kuma ana son wanka. domin yana saukaka zunubi.sai Sallah raka'a (4) kowace raka'a Fatiha (1) kulhuwa (25) Wanda ya yi wannan  Sallah Allah zai sa ya haye Siradi cikin sauki.

SALLAH TA (2).

Sallah Raka'a (2) a kowace rska'a Fatiha (1) Yaseen (1) Tabara (1) kulhuwa (1) Wanda ya yi wannan Sallah za a ba shi duk falalar da ke cikin watanni uku na Rajab. Sha'aban Ramadan.
ADDU'A:
Ana karanta addu'ar nan ta tuba a wannan daren. wato 'DU'A'UL MUJEER'. a duba 'Mafateehu' shafi na 147) don ganin addu'ar. Ya zo a ruwaya cewa: Wanda ya karanta wannan addu'a  a fararen ranakun Ramadan.za a gafarta masa zunubbansa ko da sun kai yawan digon ruwa. da ganyen bishiyoyi. da tsakuwowin tudu".(Mafatihu.147).

DARE NA (14).

Ana son yin Sadaka a daren.kuma ana son yin wanka. domin yana saukaka zunubi sai Sallah raka'a (6) kowace raka'a Fatiha (1) Izazulzlatu (30) Allah zai yaye wa wanda ya yi wannan Sallah magagin mutuwa da dacinta.

SALLAH TA (2).

Sallah Raka'a (4) a kowace raka'a Fatiha (1) Yaseen (1) Tabara (1) kulhuwa (1) Wanda ya yi wannan Sallah za a ba shi duk falalar da ke cikin watanni uku na Rajab.Sha'aban Ramadan.
ADDU'A:
Ana karanta addu'ar nan ta tuba a wannan daren.wato 'DU'A'UL MUJEER'. a duba 'Mafateehu' shafi na 147) don ganin addu'ar. A wata ruwaya an ce: karanta wannan addu'ar a fararen daren Ramadan.yana samar da waraka ga majinyaci. tana janyo biyan bashi.tana magannin talauci. tana yaye damuwa.tana kawar da bakin ciki". (Mafatihu.147).

DARE NA (15).

Ana son yi Sadaka a daren. kuma ana son yin wanka. domin yana saukaka zunubi. Sannan ana ziyarar Imam Hussain (AS) a wannan dare mai albarka.

SALLAH TA (1).

Sallah Raka'a (6) a kowace raka'a Fatiha (1) Yaseen (1) Tabara (1) kulhuwa (1) Wanda ya yi wannan Sallah za a ba shi duk falalar da ke cikin watanni uku na Rajab.Sha'aban Ramadan.

SALLAH TA (2).

Sallah raka'a (4) a raka'o'i biyun farko a karanta Fatiha (1) kulhuwa (100) a kowace raka'a. A raka'o'i biyun karshe kuma kowace raka'a a karanta Fatiha (1) kulhuwa (50) Allah zai gafartawa wanda ya yi wannan Sallah zunubbansa komai yawan su.

SALLAH TA (3).

Sallah raka'a (100) kowace raka'a Fatiha (1) kulhuwa (10) Wanda ya yi  wannan Sallah. za a aiko masa Mala'iku (10) su rika kare shi daga cutarwar makiyansa na Aljanu da mutane. kuma za a aiko masa Mala'uku (30) a lokacin mutuwarsa. su amintar da shi daga shiga wuta.
ADDU'A:

Ana karanta addu'ar nan ta tuba a wannan daren.wato 'DU'A'UL MUJEER'. a duba 'Mafateehul Jinan' don ganin addu'ar A wata ruwaya an ce: karanta wannan addu'ar  a fararen daren Ramadan.yana samar da waraka ga majinyaci.tana yaye damuwa.tana kawar da bakin ciki". ( Mafatihu.147).

Da asubahin wannan dare na (15) ga Ramadan ne aka haifi jikan Manzon Allah (S) na farko.kuma khalifan Annabi (S) na biyu.wato Imam Hassan Al-Mujtaba (AS). Abu ne mai kyau ziyartarsa a ranar.

DARE NA (16).

Sallah raka'a (12) kowace raka'a Fatiha (1) Al-Hakumu (12) Wanda ya yi wannan Sallah. Allah zai tashe shi a kabari cikin farin ciki da jin dadi.

DARE NA (17).

Daren (17) ga Ramadan dare ne mai falala da albarka.a daren ne aka yi yakin Badar mai girma. wanda shi ne nasara ta farko a tarihin Musulunci. A na son yin Sadaka a daren.kuma a ana son yin wanka. domin yana saukaka zunubi.

Sai Sallah raka'a (2) Raka'ar farko Fatiha (1) da Surar da mutum ke so. raka'a ta (2) kuwa Fatiha (1) kulhuwa (100) in mutum ya kammala sai ya yi "LA'ILAHA ILLALLAH" sau (100) Allah zai bai wa mutum ladar Hajji da Umra dubu.

DARE NA (18).

Sallah raka'a (4) kowace raka'a Fatiha (1) Inna'a'adaina (25) Allah zai yarda da wanda ya yi wannan Sallah.👏👏👏