Filing Talla

Filing Talla Ga Mai Bukata Sai Ya Tuntube Mu

Shekaru 55Masu Albarka Na Sheikh Mukthar Sahabi Kaduna

Yau 15 ga Ramadan , daya daga manyan almajiran da Allama Shaikh Ibraheem Zakzaky ya shayar da su ilimi da tarbiya kai-tsaye, Shaikh Mukhtar Sahabi Kaduna ya cika shekaru 55 da hazzalumai
An haifi Malam Mukhtar Sahabi ne a ranar 15/9/1386H, daidai da 21/8/1966 a wani gari da ake kira Gidan Madi a karamar hukumar Tangaza a jihar Sokoto.

Sunan Mahaifinsa Abubakar ne, amma mutanen yankin sun saba kiran mai suna Abubakar da Sahabi, don haka ana ce masa Malam Sahabi, a yayin da aka fi kiransa da Malam Jabbi. Gidan su Malam Mukhtar gida ne na limamai a tsawon tarihin garin nasu iyaye da kakanninsa ne limamai. Makarantan Alkur’ani ne, don haka ma bisa baiwar Allah ya sa Shaikh Mukhtar Sahabi ya sauke Alkur’ani tun yana dan shekara 6 da haihuwa a yayin da yake dan shekara 7 kuma Allah ya karbi rayuwar mahaifin nasa.

Malam Mukhtar Sahabi ya kasance na farko a cikin ya’yan mahaifinsa Malam Abubakar (Sahabi) da mahaifiyarsa Malama Asma’u. Don haka bayan rasuwar mahaifinsa a yayin da shi yake dan shekaru bakwan, an saka shi a makarantar Firamare a garin nasu inda ya kammala a nan, daga baya ya dawo hannun wani wan mahaifiyarsa a Kaduna, wanda shima ana kiransa da Alhaji Sahabi, a wajensa ya girma.

Bayan dawowarsa Kaduna, Shaikh Mukhtar ya fara karatun Sakandire a shekarar 1978, inda ya yi wata makaranta da ake kira Capital School, Kaduna. Bayan gama ta ya tafi SBRS a shekarar 1984, wanda a dalilin Gwagwarmayar addini, wani abu da ya dan faru yasa aka ce kore su a lokacin.

Shaikh Mukhtar Sahabi ya fahimci Harka Islamiyya ne tun a shekarar 1980, lokacin bai fi shekaru 14 a duniya ba, a wajen wani taron dalibai (IVC) irin wanda aka saba gabatarwa a wancan lokacin, a yayin yana dan Sakandire. Sai dai tun a lokacin ya amshi Harkar hannu bibbiyu, ta yadda kai tsaye ya juyar da dukkan akalar rayuwarsa zuwa ga Harkar addini. Dama ya taso ne a gidan addini, don haka sai ya zama a Sakandiren ma shi ke limancin Sallah, sannan ya baiwa dalibai Musulmi karatun littafan addini tun a sannan.

Bayan fahimtarsa da Harkar Musulunci, da yadda dalibai suka ga ya tsaya kyam da harkokin addini, sai wasunsu suka rika kiransa da suna Khumaini. Wato a wajensu duk wanda ya tsaya kyam a kan harkokin addini ya cancanci a kira sa da sunan Imam Khomeini (QS).

Shaikh Mukhtar Sahabi ya rika yi wa addini hidima a sakandire, ta yadda da an gan shi an ga Musulunci ne, don haka ne ma har ya samu rabautar Musuluntar da wasu da a da ba Musulmi ba har mutum uku, daga cikinsu akwai wata mace Baturiya mai suna Lizly, wanda ya maida sunanta zuwa Zainab bayan Musuluntar nata. A yayin da mutane da yawa kuma suka fahimci Harkar Musulunci ta hanyarsa saboda kyawawan dabi’unsa da riko da addininsa.

Bayan koran da aka musu daga jami’ar A.B.U Zaria a 1984, mafi yawan yan uwan sun komo Kaduna ne suka nemi Polytechnic. Shima Shaikh Mukhtar haka ya yi, inda ya nemi ‘admission’ a Kaduna Polytechnic ya fara karanta ‘Food Technology’ a shekarar 1985. Wanda saboda ayyukan Harka da suka tsayu da shi a lokacin, sai da aka kara musu shekara guda a kan shekarun karatun nasu kafin gamawa.

Shaikh Mukhtar Sahabi ya yi aure ne a ranar 27/10/1409H daidai da 31/5/1989 kimanin shekaru 30 da suka gabata. Matarsa guda daya, Malama Jamila Auwal. Sun haifi ‘Ya’ya 9, a yayin da biyu daga cikinsu Allah ya musu rasuwa, yanzu akwai bakwai raye da suka hada da Ukhasha, Asma’u, Maryam, Mahdi, Husaini, Fatima da Zainab. Biyun da suka rasu sune Zainab da kuma Narjees.

Tsayuwar Shaikh Mukhtar Sahabi a gwagwarmayar addini wani abu ne da ‘yan Gwagwarmayar basu da bukatar sai an musu bayani a kansa, domin kuwa duk sun san wane ne shi. Shaikh Mukhtar Sahabi ta kai ma ga ana kiransa da Uban ‘Yan Chaji, saboda tsananin dakewarsa a kan addini da yadda yake shajja’a yan uwa a kan Gwagwarmaya.

Ya kasance haziki, ma’abocin basira da fasahar iyar da magana. Da wuyar gaske Malam Mukhtar Sahabi ya maka bayani a kan wani abu a addini ya zama baka fahimce shi ba, har ma akan kira shi da wani lakabi na ‘Ayatullahi Bayani’, wato don tsabar iya bayaninsa. Ya siffantu da dabi’ar tsafta wanda ya bayyana cewa ya tasirantu da tsaftan ne daga rayuwar Jagoransa (H).

Mutum ne mai hakuri sosai da cutarwar da ake masa kai tsaye, amma tana da dabi’ar rashin hakuri ko juriya a kan duk cutarwar da zata shafi mutuncin addini ko Harka Islamiyya da Jagora.

Mutum ne shi mai gaskiyar zance, duk abin da ya fada yana nufin abin ne har a zuciyarsa, a yayin da a kan idanunmu mun ga dakewarsa a Gyallesu a lokacin harin sojojin Nijeriya a gidan Jagora (H). Harin ya fara aukuwa ne a Husainiyya da rana, a yayin da Malam Mukhtar Sahabi yana Abuja ya wakilci Jagora (H) a wajen Mauludin Shehu Danfodiye da aka yi a ranar Asabar din, amma daga Abuja din da ya ji labarin an kai hari Husainiyya kai tsaye ya wuto Zariya.

Kamar idanuna na kallon safiyar Lahadi, Su Malam Hammad, da su Zuhair sun dibo dogayen masu za su tunkari soji, su Malam Ƙasim sun tsare su suna rarrashinsu a kan su dakata sai babu yan uwa tukunna, Malam Mukhtar yana zuwa wajen bai tsaya komai ba ya fizgi mashi guda a hannun daya daga cikinsu ya nufi inda sojojin suke yana kokarin sauke wajibinsa. Tun a asubahin ranar shi ke raba ma yan uwa wajen da za su tsare don kar soja su kai ga gidan su Malam (H). Ganin karshe da na masa shine sanda yake cewa yan uwa, kun ga sun raunata mu ta gaba, akwai yiwuwar su zagayo ta baya, don Allah mu dake, a wasunmu su zo mu tare bayan nan ko da za su zagayo. Ba a jima da hakan ba kuwa sai ga shi sun zagayo ta bayan. Ban san halin da yan uwan da suka tare bayan suke ciki ba.

Tun daga wannan harin na Gyallesu, yau shekaru fiye da uku ba a san ina sojojin Nijeriya suka kai Shaikh Mukhtar Sahabi ba, domin shi babu wani da ya ganshi bisa tabbacin an harbe shi, don haka ana kyautata zaton yana daga cikin ‘yan uwan da sojojin suka kama suka boye su a wani waje boyayye har yau din nan. Allah Ya amintar da su a duk inda suke.

A irin wannan rana ta haihuwar babban jikan Manzon Allah (S), Imam Hasan Almujtaba (AS), muna kuma taya Shaikh Mukhtar Sahabi da iyalai da masoyansa murna da kasancewar ta a matsayin ranar haihuwarsa. Muna rokon Allah albarkacin Iman Hasan (AS), Ya kubutar da Jagoranmu da su Malam Mukhtar Sahabi tare da dukkan yan uwa daga kangin azzalumai

Kaduna Pree 
7/5/2020

A madadin yan uwa na dairan kaduna da keway muna taya iyalain Mal Mukthar murna da wannan ranar

Post a Comment

0 Comments

Close Menu