Filing Talla

Filing Talla Ga Mai Bukata Sai Ya Tuntube Mu

Shugaban kasar Turkiyya ya yi Allah wadai da kisan da 'yan sanda suka yiwa wani bakar fata a Amurka

Shugaban kasar Turkiyya Recep Tayyip Erdoğan ya yi tir da Allah wadai akan kisan wani bakar fata George Floyd sanadiyar ukubar 'yan sandan Minneapolis a Amurka.

Shugaba Erdogan ya bayyana cewa "Muna masu matukar yin Allah wadai ga irin wannan dabi'ar da ta sabawa hallayar dan adam" 

Shugaba Erdoğan, ya yi sharhi a shafinsa ta Twitter da harshen Ingilishi akan ukubar 'yan sanda da ya haifar da mutuwar Floyd.

Inda yake bayyana cewa, 'Mutuwar Floyd sanadiyar ukubar da ya fuskanta daga hannun 'yan sanda tsari ne na nuna wariyar launi fata da dabi'ar ra'ayin facism. Wannan rashin adalcin bai tsaya akansa kawai ba har ga duniya baki daya. Muna masu kyamar wannan dabi'ar da ya sabawa dabi'ar dan adam. A koda yaushe, a ko ina Turkiyya za ta kasance mai kalubalantar dukkanin yunkurin cin zarafin dan adam'

A yayinda Erdoğan ke tunatarwa da hadisin Manzon Allah Annabi Muhammadu (SAW) wanke ke bayyana cewa "Fari ba shi da fifiko akan baƙar fata. Baƙar fata ma ba shi da wata fifiko a kan farar fata."

Ya kara da cewa sabanin nuna wariyar jinsi, launin fata, harshe da addini zamu cigaba da gwagwarmayar kare hakkoki da mutuncin bil adama.

Shugaba Erdoğan ya mika sakon ta'aziyya ga iyalai da 'yan uwan George Floyd. Inda ya jadadda sanya ido domin tabbatar da an hukuntar da wadanda suka aikata laifin.

Post a Comment

0 Comments

Close Menu