Filing Talla

Filing Talla Ga Mai Bukata Sai Ya Tuntube Mu

Wadanda Suka Warke Daga COVID-19 A Afirka Sun Kai 58,000


A nahiyar Afrika, alkaluman mutanen da aka tabbatar sun kamu da cutar COVID-19 ya kai 139,000.

Adadin kuma mutanen da suka rasa rayukansu sakamakon cutar sun kai 3,941, kana wadanda suka warke sun haura 58,000 kamar yadda hukumar dakile yaduwar cutuka ta Afrika, CDC ta sanar.

Kawo yanzu dai adadin mutanen da cutar ta kashe a fadin duniya, ya doshi 370,000 tun bayan bullatar a watan Disamban bara a kasar China.

Ya zuwa wannan Lahadin, alkalumman mutanen da suka kamu da cutar a duniya ya kai miliyan shida da dubu saba’in da biyar da saba’in, (6.075.070), a cikin kasashe 196 na duniya.

A alkalumman da kamfanin dilancin labaren AFP, ya fitar wadanda suka dogara da bayannan da hukumomin kasashen duniya ke fitarwa akwai kuma mutane miliyan 2,502,600 da suka warke.

Post a Comment

0 Comments

Close Menu