Filing Talla

Filing Talla Ga Mai Bukata Sai Ya Tuntube Mu

Wajibi Ne Duniyar Musulmi Su Girmama Ranar Qudus


Fatima Muhammad Ahmad✍️
Kaduna Press

Bai kamata musulmi su bari wasu daga cikin gwamnatocin da suka sayar da kawunansu cikin hali da yanayi na shirun da suka haifar a hankali a hankali su sanya batun Palastinu ya narke shi kenan ya zamanto lamarin da aka mance da shi ba.

Bai kamata a mance da irin ha’inci da gwamnatocin da suka hada baki da haramtacciyar kasar Isra’ila sannan kuma suka mai da Palastinawa suka zamanto ragunan layyansu suka aikata ba, sannan kuma a bar lamari haka kawai ba.

Wannan lamari ba karamin lamari ba ne Ku girmama Ranar Kudus sannan kuma ku dauke ta a matsayin rana mai girma.

Ko da yake kafafen watsa labaran duniya ba sa fadin abubuwan da aka gudanar (a wannan ranar); to kada su yi hakan.

Wadannan mutan(Palastinawa) da suke Palastinu, suna gaya mana cewa irin wadannan take da kuke dagawa, da irin wannan kasantuwa ta ku da irin matsayar da kuke dauka wadanda suke nuni da irin niyya da azama ta gaskiya da kuke da ita – sukan sanya mu jin karfi da kuma kara mana karfin tsayin daka.

Bai kamata Palastinawan da suke gidajen yarin (yahudawan sahyoniya) su ji cewa su kadai ba ne, don su sami karfin gwuiwan tsayin daka.

Wannan Mutane maza da mata da suke fuskantar hare-hare da cin mutumcin ‘yan daban yahudawan sahyoniya a lunguna da titunan garuruwan Baitul Mukaddas da Zirin Gaza da sauran garuruwan Palastinawa da aka mamaye, wajibi ne su ji cewa lalle muna tare da su, don su sami damar ci gaba da gwagwarmaya.

Ko da yake gwamnatoci su ma suna da wani nauyin da ya hau kansu. Mai girma du da sun sai da lahiran su, sun sai duniya……..

Post a Comment

0 Comments

Close Menu