Hukumar sa ido ta masallatan Makka da Madina na da tsari na ta gindaya da ya fayyace yadda ake bai wa limamai da ladanai damar kira da yin sallah. Majalisar ta kuma fito da matakan zaben limaman da ladanan kamar haka:

Matakin farko shi ne masu takarar neman limami ko ladani dole ne su kasance 'yan kasar Saudiyya kuma ba su gaza shekara 30 da haihuwa ba.
Sannan kuma dole 'yan takarar sun zama suna da digiri na biyu a daya daga cikin jami'o'in da ke Saudiyya.
Dole ne ladani ya nuna irin sanin da yake da shi dangane da kiran sallah a littafan musulunci - Qur'ani da Sunnah
Abin so ne liman da ladani su zama masu zazzakar murya tare da iya rera karatun.
Dole ne mai takarar limanci ya zama yana da haddar AlQur'ani sannan ya zama yana da murya da tajweedi dai-dai gwargwado.
Yadda ake nada liman da ladan
Nadin limami zai kasance ne bayan da amincewar majalisar ministoci bisa shawarar shugaban masallatan Makka da Madina.
Dole nadin mai kiran sallah ta samu sahalewar shugaban masallatan Makka da Madina bisa amincewar kwamitin da shugaban kasa ya kafa da suka kunshi limamai da ladanai.
Nadin limamai da ladanai na zuwa karshe ne bayan da suka bar aiki ko kuma aka samu gazawar ci gaba da aiki sakamakon rashin lafiya saboda tsufa.
Wa'adin limamai da ladanai
Hakkin mallakar hotoGETTY IMAGES
Tsawon lokacin da liman da ladan ke yi yana gudanar da sallah a Saudiyya shi ne shekaru hudu. Amma za a iya sabunta musu wa'adin. Har wa yau, shi ma ladani wa'adinsa shekaru hudu ne amma za a iya sabunta masa bayan da shugaban masallatan biyu ya nemi a yi hakan.

Ayyukan Majlaisar Limamai da ladanai

Majalisar limamai da ladanai ta masallatan Makka da Madina ba ta amince da liman ko ladan ya halarci taron gabatar da mukala a wajen Saudiyya ba ko kuma su gabatar da mukala ba tare da iznin hukuma.
Majalisar dai ce ke da alhakin nada da kuma tantance 'yan takarar domin zaben wadanda suka yi fice.
Har wa yau, majalisar ce take zabar wadanda za a nada su a matsayin limaman masallatan biyu a watan azumin Ramadan.

Safuwan Sp harun
Kaduna press