Az~Zahra Badamasi Ishaq✍️
Kaduna Press

Samun nasarar da Manzon Allah (s) ya yi bayan hijirarsa daga Makka zuwa Madina, da kuma irin karbar da mutanen Madina suka yi masaya sanya kafiran Makkan cikin halin damuwa da kuma kara gaba da shi. Don haka suka fara tunanin hanyar da za su bi wajen kawo karshen wannan addini na Musulunci da kuma wanda ya kawo shi (Annabi). Don cimma wannan manufa, kafiran Makkan da 'yan koransu suka fara kawo hare-hare ga yankunan da suke kusa da garin Madinan da kuma lalata kayayyakin gonakin musulmi da kuma diban 'ya'yan itatuwan bishiyoyin musulman.

Ganin irin wannan shiri na makirci da kafiran suke wa musulmin da kuma musuluncin ya sa Manzon Allah (s) ya kuduri aniyar kai hari wa wasu hanyoyin da kafiran suke samum kudaden shigan da suke amfani da su wajen kulla irin wadannan makirce makirce. A bangare guda kuma kafiran Makka suna nan suna ta shirye-shiryen soji don kawo gagarumin hari wa musulmi da kuma murkkushe su. Kafiran dai sun iya tara rundunar soji da kai mutane 1000, da ta hada da rakuma 700 da kuma dawaki 100, don aiwatar da wannan kuduri na su.

Koda wannan labari ya zo wa Manzon Allah (s) sai shi ma ya shirya rundunarsa ta mutane 313 da nufin fuskantar kafiran, inda suka fito daga garin Madinan don taryar kafiran a waje. Koda sojojin musulman suka iso wani guri da ake ce ma Badar, sai Manzon Allah (s) ya umurce su da dakata a gurin su jira isowar sojojin kafiran. Koda kafiran suka iso wajen sai Manzon Allah (s) ya tura Ammar bn Yasir da Abdullah bn Mas'ud don su je su leko asirin kafiran da kuma karfin da suke da shi don a san yadda za a bullo musu. Inda wadannan sahabbai suka je kuma suka dawo da labarin da suka samo.

Kafin a fara wannan yaki dai Manzon Allah (s) ya mika tutan rundunarsa ne ga Amirul Muminina Aliyu bn Abi Talib (a.s).

Wannan yaki dai na Badar an fara shi ne a ranar 17 ga watan Ramalana shekara ta biyu bayan hijira. A wancan lokacin dai, larabawa suna da wani tsari na yaki da suke bi, shi ne kuwa kafin a fara yakin wasu dakaru sukan fito su gwabza tsakaninsu. Don haka a yakin na Badar din ma hakan ne ya faru.

Koda bangarorin biyu (wato bangaren gaskiya da shiriya karkashin jagorancin Manzon Allah (s) da kuma bangaren karya da bata karkashin jagorancin Abu Sufyan) suka fuskanci juna sai wasu kafirai guda uku, wato Walid, Shaybah da kuma Utbah, sai wasu sahabbai Ansarawa guda uku suka fito, sai suka ki amincewa da su suka ce ai ba sa'oinsu ba ne. Sai Manzon Allah ya umurci Ali bn Abi Talib, Hamzah da kuma Ubaydah da su fito su tunkare su. Inda ya ce wa Aliyu ya kama Walid, Hamzah kuwa ya kama Shaybah shi kuma Ubaydah ya kama Utbah. Koda aka fara gwabzawa, nan take Aliyu ya kashe kashe Walid, Hamzah ma ya sare Shaybah, shi kuwa Ubaydah Utbah ya ji masa ciwo, nan take Aliyu da Hamzah suka kawo masa dauki, suka karasa Utbah.

Ta haka ne sojojin Musulmi suka fara samun nasara, tsoro da fargaba kuma ya shiga zukatan dakarun kafirci, inda wuri ya rude, daga karshe dai musulmi suka sami nasara, suka kashe da dama daga cikin kafirai da taimakon Aliyu bn Abi Talib wanda ya kashe mafi yawa daga cikin kafiran da aka kashe a yakin. Kafirai suka watse suka gudu musulmi suka bi su suka dibi ganima da kuma fursunonin yaki suka dawo gida.

Wannan dai shi ne nasarar farko da musulmi suka samu a bangaren soji akan kafirai.

Kaduna Press:
Munatl Taya Al'umma Murnar Ranar 17 Ga Watan Ramadan.