Fatima Muhammad Ahmad✍️
Kaduna Press

Girmama Halin Da Sanin Mutunci ka:

Hakika mafi girman da kuma daukakan abin da mutum zai iya mallaka a rayuwarsa shi ne hali da kuma mutumcin kansa, hakan kuwa wata amana ce da take a kan wuyansa wacce Allah Madaukakin Sarki Ya daukaka shi da ita. Sannan kuma Ya haramta masa ha'intar kansa ko kuma kaskantar da ita da kuma ha'intar abin da Ya ba shi na kwarewa.

Imam Sadik (a.s.) ya yi bayanin wannan al'amari mai muhimmanci cikin fadinsa ce wa:

"Allah Madaukakin Sarki Ya bar (halalta) wa mumini dukkan kome in ban da wulakantar da kansa".

Lalle babban nauyin da ke kan mutum dangane da kan kansa shi ne ya kiyaye abin da zai zubar masa da mutumcinsa cikin al'ummar da yake raye a ciki. Don kuwa ayyukansa suna nan a kan idanuwan al'umman da yake tare da su, kada ya aikata wani abin da zai zubar masa da mutumcinsa ta yadda shi ma da kansa zai yi dan da-na-sanin wannan aiki.

Kamar yadda hanyoyin girmama zatin dan'Adam da kuma samar da daukaka ga mutumcinsa suke da yawa, haka ma hanyoyin ha'intar kai da kuma zubar da mutumci suke da yawa....

Misali, karya da ta'addanci a kan al'umma, ya kan haifar da wulakantar da kai, haka ma aikata muggan ayyukan da suka saba wa dabi'u na kwarai, yarda da wulakanci ko don saboda neman kudi, jin dadi ko matsayi, duk hakan suna haifar da wulakanci, munafunci, tsoro.....da dai sauransu.

Haka nan kuma jin kaskanci da kuma sanya wa zuciya tunanin gajiyawa ta rashin iya aikata wani aiki, hada kai cikin aikin alheri da kuma hidima ga al'umma, duk hakan sukan kashe zuciyar mai yin su.
Don kuwa Allah Madaukakin Sarki Ya arzurta dukkan 'yan'Adam da karfi da kuma iyawa, don haka ya rage musu ne kawai su yi amfani da su wajen cimma manufarsu ta rayuwa. Don haka ba ya halalta gare su da su yi wasa da karfi da ikon da Allah Ya ba su.....

Hakika Allah Madaukakin Sarki ba Ya haramta wa bayinSa ni'imominsa....wasu suna da karfin fahimtar ilimin magani, wasu kuwa ilimin yare, wasu kuma karfin kirkiro abubuwa suke da shi. Sannan wasu kuma karfin kasuwanci suke da shi, wasu kuma na ayyukan hannu suke da shi, wasu kuma na iya gudanar da mulki suke da shi, sannan wasu kuma karfin siyasa da ayyukan soji suke da shi....da dai sauransu.

Haka lamarin yake, don kuwa dan'Adam yakan gano iko da karfin da Allah Ya yi masa ne ta hanyar gwaji, don haka kada mutum ya wulakantar da abin da Allah Ya arzurta shi na daga karfi da kuma iko.

Sau da dama mutane sukan wofantar da kwarewa da kuma karfin tunani da kuma na aiki da Allah Ya ba su saboda yanke kauna da kuma jin gazawa. Ta hakan sai ka ga sun lalata karfin da suke da shi da kuma hana kansu hakkin da ya dace da ita da kuma hana ta damar ci gaba da kuma samun nasara.

Lallai babu shakka, yarda da kai, buri da kuma kokari sukan karfafa rai da kuma ba ta dukkan abin da take bukata wajen ci gaba da kuma gudanar da ayyukanta kamar yadda ya dace. Don kuwa dogaro ga Allah da kuma yarda da kai, mabudi ne na aiki da kuma cimma nasara a rayuwa.

Please 🙏 Share It To Youth's 🌹