Filing Talla

Filing Talla Ga Mai Bukata Sai Ya Tuntube Mu

Zuwa Ga Matasa 7

Fatima Muhammad Ahmad✍️
Kaduna Press

Gaskiya da Wajibi A Tsakanin Al'umma

Dukkan wata halitta a wannan duniya tamu, tana da wata siffa ta taimakekkeniya da 'yan-'uwanta, tana bayarwa da kuma karba daga 'yar'uwan nata. Misali, mutum, dabbobi, tsirrai da dabi'a, duk suna jujjuya amfani tsakaninsu, da suka hada da iskar "oxygen" da "carbondioxide", abinci, haske, ruwa. da dai sauransu.

Haka shi ma mutum, yana rayuwa ne cikin iyali da al'ummarsa, yana alaka da sauran mutane kana kuma suna jujjuya amfanoni a tsakaninsu. Don haka yana da hakkoki a kan iyali da kuma al'ummarsa, kamar yadda su ma suke da hakkoki a kansa. Ko wane mutum yana da hakki, yana kuma da wajiban da suka hau kansa, to amma wannan daidaituwa ta al'ummance da dokoki na al'umma ba za su taba tabbatuwa ba kana kuma zaman lafiya da kwanciyar hankali ba za su samu ba, har sai an kiyaye wadannan al'amurra.

Hakika duk wanda ya bukaci wani abin da ba hakkinsa ba ne, to ba makawa yana zaluntar sauran mutane ne, don kuwa so yake ya bautar da al'umma. A sabili da haka ne al'umma suke ki da kuma jefar da shi.

Dan'Adam yana da hakkin rayuwa, kamar yadda kuma rayuwar hakkinsa ce, haka nan ma samar masa da abubuwan da rayuwar take bukatuwa da su. sannan kuma yana daga cikin hakkinsa a bude masa hanyoyin ayyuka da kuma 'yancin samun abin hannu da kuma mallaka. kuma hakkinsa ne ya samu nasa rabon na albarkatun kasar da yake raye cikinta.

Muna iya ganin hakkokin dan'Adam a fili cikin fadin Allah Madaukakin Sarki:

"Kuma kasa ya aza ta domin talikai". (Surar Rahman, 55: 10)

Don haka an sanya kasa ne don kowa da kowa ya amfana da ita, kuma ba ya halalta ga wani mutum ya ajiye ta a matsayin kayansa kawai ya

hana saura amfanuwa da ita. Dan'Adam wani sashi ne na wannan al'umma, yana da hakkin amfanuwa da dukkan abubuwan da suke cikin al'ummarsa.

Hakika kange amfani da alherorin da suke cikin kasa ga wata al'umma ko kuma kungiya da kuma haramta wa wata, zalunci ne da kuma gaba da dokokin rayuwa da kuma ka'idojin adalci.... Alkur'ani mai girma yana tabbatar da wannan ka'ida cikin fadinSa Madaukakin Sarki:

"Lallai Allah Na yin umurni da adalci da kyautatawa". (Surar Nahl, 16: 90)

Don haka "mutane daidai suke kamar hakwaran matsefin kai", kamar yadda Manzon Allah (s.a.w.a.) ya fadi.

Lallai babu makawa a duk lokacin da mutane suka yi shiru kan zalunci da kuma babakeren da ake musu, to cutarwar za ta koma ga kowa da kowa ne, daga karshe sai ya zamanto wata kungiya ta azzalumai ta hau kan dukkan al'umma da kuma raunana ta.

Don haka, kamar kowane mutum yake kokari wajen sama wa kansa 'yanci, haka nan ya za ma wajibi a kansa ya yi kokari wajen samar wa sauran mutane ma, kada ya takaita shi ga kansa kawai.

Sannan kuma yana daga cikin hakkin dan'Adam ya rayu cikin tsaro da kwanciyar

hankali, shi da dukiyarsa da kuma dukkan abin da ya mallaka, hana shi wannan 'yanci kuwa zalunci da babakere ne wanda mai aikata hakan ya cancanci azaba. Kana kuma kamar yadda hakan ya zamanto 'yancinsa, haka nan ma ya zamanto 'yancin wasunsa ne, don haka a duk lokacin da ya yi wasa da tsaron lafiyar wasunsa, ko kuma ya aikata wani abin da zai tsoratar da su, ko kuma ya haifar da rashin tabbas da kwanciyar hankali a cikin mutane, to ba makawa ya zamanto abokin gaban al'umma, kuma hakan ma wasa ne da tsaron kan kansa shi ma.

Manzon Allah (s.a.w.a.) ya tabbatar da ka'idar tsaro da kwanciyar hankalin al'umma cikin fadinsa cewa:

"Musulmi dan'uwan musulmi ne, don haka kada ya cutar da shi, ko ha'intarsa ko ya fadi mummunar magana dangane da shi. Sannan kuma jininsa ba ya halalta a gare shi, haka ma dukiyarsa sai da yardarsa".

Daraja da daukakar dan'Adam tana ga mutumci da karamarsa ne, don haka shari'ar Musulunci ta haramta giba, bata suna, yada kararraki da zubar da mutumcin mutum ta hanyar magana ko aiki ko kuma ta hanyar bincike da bayyana asirin mutum da dai sauransu.

Wannan doka ta Musulunci tana wajabta wa mutum girmama mutumcin sauran mutane, kan
____________
1- Al'Ya'akubi / juzu'i na 2 / hudubar ban-kwana /shafi na 110/ Dar Sadr - Beirut.

kuma ba ya halalta ya keta hurumin sauran mutane. Allah Madaukakin Sarki Yana ce wa:

"Ya ku wadanda suka yi imani! Kada wadansu mutane su yi izgili game da wadansu mutane, mai yiwuwa ne (abin yi wa izgilin) su kasance mafifita daga gare su (masu izgilin), kuma wadansu mata kada su yi izgili game da wadansu mata mai yiwu-wa ne su kasance mafifita daga gare su. Kuma kada ku aibanta kanku, kuma kada ku jefi juna da miyagun sunaye na lakabobi. Tir da suna na fasicci a bayan imani. Kuma wanda bai tuba ba, to, wadannan su ne azzalumai. Ya ku wadanda suka yi imani! Ku nisanci abu mai yawa na zato. Lalle sashen zato laifi ne. kuma kada ku yi rahoto, kuma kada sashenku ya yi gibar sashe. Shin dayanku na son ya ci naman dan'uwansa yana matacce? To, kun ki shi (cin naman). Kuma ku bi Allah da takawa. Lalle Allah Mai karbar tuba ne, Mai jin kai". (Surar Hujurat, 49: 11-12)

Haka nan kuma mutum yana da wasu hakkoki a kan al'umma da kuma kasarsa, wadanda gwam-nati ce take daukan mafiya yawa daga cikinsu; wadannan hakkoki sun hada da bayar da ilimi, tarbiyya, kula da samar da tsaro, kiwon lafiya da dai sauransu.

Kamar yadda kuma kasa da al'umma suke da wasu hakkoki a kan mutum, kamar su kiyaye maslahohin al'umma da kuma kare su, bugu da kari kan wajiban da suka hau kansa wadanda doka ta yi bayaninsu, wadanda matukar dai bai kula da kuma kiyaye su ba, to rayuwar al'umma za ta kasance tana fuskantar matsaloli da kuma rugujewa. A irin wannan hali shi ma ba zai tsira daga bala'in da zai fada wa sauran al'umma ba.

Please🙏Share It To Youth's🌹

Post a Comment

0 Comments

Close Menu