Fatima Muhammad Ahmad✍️
Kaduna Press

Ya Ya Za Mu Fahimci Rayuwa? Kuma Ya ya Za Mu yi Mu'amala Da Ita?

Wannan rayuwa da muke cikinta.ya ya za mu iya fahimtarta?. kana kuma ya ya za mu yi mu'amala da ita? 

Rayuwar dan'Adam ita ce ayyukan jiki, tunani da na ruhi da mutum yake aikatawa tun daga haihuwarsa har zuwa mutuwarsa. Kuma ta hakan ne yake tabbatar da samuwarsa da kuma cika zati, ruhi da kuma yanayinsa. Yakan cika hakan ne kuwa ta hanyar abubuwan da ya mallaka, na daga rayuwa, hankali, karfin yanayin abubuwan da suke kewaye da shi, jin dadi da kuma ciwo, gano abubuwan halitta da hankalinsa yake yi, da dai sauransu.

Hakika mun kasance muna ci da sha, muna sa tufafi, muna wasa da jin dadin kyawawan abubuwa, muna jin soyayya da kiyayya, farin ciki da bakin ciki, jin dadi da kuma jin zafi, muna dariya da kuka, mukan yanke kauna kan al'amura da kuma burace-burace.

Sannan kuma mukan yi tunani da kuma kirkiro abubuwa, mukan gano sabbin abubuwa sannan kuma mu sanya wasu, kuma mukan yi bayanin abubuwan da suke damunmu ta hanyar magana, rubutu, wake, farin ciki da kuma bakin ciki.

Kana kuma mukan gano abubuwan da suka fita daga wannan duniya tamu ta hanyar hankali da kuma tunaninmu, muna masu tunanin girmansu da kuma yadda aka samar da su. Kuma mukan gano ka'idojin samuwa da kuma Wanda Ya samar da ita.

Hakika mun kasance muna tunani, muna ji, muna aiki, kuma mukan tsara rayuwarmu da tunani da kuma shu'urinmu, da kuma ayyukan da suke fitowa daga gare mu.

Mu mun kasance jiki, ruhi da kuma hankali ne wadanda aka arzurta mu da su. Mu muke sana'anta rayuwarmu kamar yadda mai zane yake zana hoto, rayuwar kowanne daga cikinmu hotonsa ne na zati, to a cikinmu wane ne yake so hotonsa (zatinsa) ya kasance abin kyama.

Hakika rayuwa ba wai jin dadi da annashuwa ba ce kawai, face dai tana hade da abubuwan bakin ciki da dacin rai kuma. Ita ba wai kawai sakaka take ba, face dai ita nauyi ce, nauyi ce a gaban Allah Ta'ala, nauyi ce a gaban al'umma da kuma mutanen da muke rayuwa da su. Sannan kuma nauyi ce a gaban dokoki, mutumci da kuma samuwa.

Allah Madaukakin Sarki Yana cewa:

"Sa'an nan lallai ne Muna tambayar wadanda aka aika zuwa gare su, kuma lallai Muna tambayar Manzannin".(Surar A'araf,7: 6)

Manzon Allah (s.a.w.a.) yana cewa:

"Dukkanku makiwata ne, kuma dukkanku abin tambaya ne kan abubuwan da aka ba ku kiwonsu".

Hakika Ubangijin halitta Ya yi bayanin dabi'ar rayuwa, kuma Yakan buga misalai wadanda za su kusanto da lamurra zuwa ga hankulanmu. Ya yi bayanin cewa ita (rayuwa) aiki ne na girma, daukaka da kuma kamala, kana kuma daga baya ta zamanto abin jefarwa da kuma karewa. To haka rayuwar ko wane mutum a wannan duniya take.

"Ka buga musu misalin rayuwar duniya, kamar ruwa ne wanda Muka saukar da shi daga sama, sa'an nan tsirin kasa ya garwaya da shi, sa'an nan ya wayi gari dudduga, iska tana shikar sa. Kuma Allah Ya kasance Mai yawan ikon yi ne a kan dukkan kome". (Surar Kahf, 18: 45)

Don haka rayuwa, duk da irin kawa, kyau, jin dadi da annashuwan da ke cikinta, wata aba ce samammiya kana mai karewa, kamar yadda tsirrai sukan girma su yi fure masu kyau, amma daga baya su yi 'ya'ya kana su bushe iska ta debe su.

A lokacin da wannan marhala ta rayuwar mutum ta kare, sai kuma wata sabuwar marhala ta rayuwar tasa ta kunno kai, ita ce kuwa rayuwar lahira. Wannan kuwa ita ce dawwamammiyar rayuwa. duniyar da babu wani canji ko gushewa a cikinta. Duniyar ni'ima, kyau da kuma jin dadi, ko kuma duniyar tabewa da kuma azaba.

Hakika abin da ke tabbatar da makomar mutum a wancan duniyar, shi ne yanayin ayyuka da kuma akidarsa a wannan duniya, kamar yadda kokarin dalibi yake tabbatar da sakamakon jarrabawarsa da kuma ci gaban karatunsa.

Lallai a wannan rayuwa ce mutum yakan share fagen rayuwarsa ta lahira, kamar yadda duniyar mahaifa take share fagen rayuwa duniya.

Alkur'ani mai girma ya yi mana bayanin wannan hakika cikin fadinSa Ta'ala ce wa:

"Wanda ya kafirta, to, kafircinsa na kansa, kuma wanda ya aikata aikin kwarai, to, saboda kansu suke yin shimfida". (Surar Rum, 30: 44)

Don haka ne dokokin Ubangiji suka zo don tsara ayyukan dan'Adam da kuma yanayin rayuwarsa.

Abu ne mai yiwuwa mutum ya bi sha'awace-sha'awacensa, jin dadi da kuma annashuwa, ko kuma ji-ji da kai, jahilci ko kiyayya su sami iko a kansa, ta haka sai rayuwa ta kasance wata hanya ce ta biya sha'awa da jin dadi a gare shi. Ko kuma ta kasance hanya ce ta aikata laifuffuka da yada fasadi a bayan kasa da kuma bauta ga jin dadin duniya saboda son zuciya da kuma ji-ji da kai.

Hakika Mahaliccin rayuwa Ya bai wa mutum ita (rayuwa) ce don ya rayu cikin kwanciyar hankali da jin dadin abubuwan jin dadin cikinta da kuma kawaice-kawaicenta, gwargwadon yadda dokokin kiyaye rayuwa da kuma kyautata dabi'u suka tanadar. Ta yadda zai iya tabbatar da alheri a kansa da kuma al'umma da yake rayuwa a cikinta.

Babu shakka, a lokacin da mutum ya yi kuskuren fahimtar rayuwa, to lallai zai cuci rayuwarsa da kuma ja-gorantarta zuwa ga halaka, kuma da wuya ya iya gane wannan kuskure na sa sai bayan gushewar lokaci.

Don da yawa daga cikin mutane, sha'awoyi, son zuciyarsu da kuma gururi sun kai su zuwa ga halaka da kuma nadama, hakan kuwa bayan kurewar lokaci.

Rayuwar irin wadannan mutane ta kare a gidajen yari daban-daban, kashe kai, kamuwa da muggan cututtukan jima'i (irinsu ciwon AIDS da dai sauransu), shan muggan kwayoyi, damuwa, tabewa da dai sauransu.

Cibiyoyin kididdiga da bincike irin su asibitoci, cibiyoyin lafiya da kuma na muggan laifuffuka sun tabbatar da adadi mai yawan gaske na faruwar irin wadannan laifuffuka a tsakanin al'umma.

Hakika rayuwarmu kyauta ce ta Ubangiji Mai rahama, don haka dole ne mu yi mu'amala da rayuwarmu daidai da dokokin kiyaye lafiya da kuma rayuwa. Hakan kuwa su ne dokokin Ubangiji, Wanda Ya haramta mana duk wani abin da zai cutar da mu, sannan kuma ya halalta mana dukkan alherori da jin dadin da suke da amfani a gare mu.

Akwai hanyoyi na fahimtar rayuwa, don haka wajibi ne mu koma gare su da kuma dogaro da su. Wadannan hanyoyi kuwa su ne:

Littafin Allah da kuma shiryarwar Annabci; wadannan abubuwa guda biyu suna mana cikkakken bayanin rayuwa da kuma hanyoyi da tafarkin shiriya cikin rayuwarmu. Don haka dole ne mu karanta su tare da tunani da kuma cikakkiyar fahimta, don mu san abin da ke cikinsu na alheri da kuma hikima.

Mabubbuga ta biyu na fahimtar rayuwa shi ne ilimi da bincike-bincikensa. Hakika ilimi ya arzurta mu da masaniya da kuma fahimta, ta yadda ya iya bayyana mana abubuwa masu cutarwa da kuwa masu amfanarwa. Sannan kuma wadannan abubuwa da ilimi ya tabbatar da su sai suka yi dai-dai da abin da Alkur'ani mai girma ya tabbatar na haram da halal.
Hakika ilimi ya gano hadarin da ke tattare da giya, muggan kwayoyi, zinace-zinace, cin kudin

ruwa, haka nan kuma ya gano fa'idar tsabta, soyayya, sada zumunci tsakanin 'yan'uwa da kuma tasirin da yake da shi wajen kiyaye zaman lafiyan al'umma, da kuma tasirin imani wajen sa'adar dan'Adam, tabbatuwa cikin dabi'u na kwarai, tsira daga damuwa da kuma muggan laifuffuka.....da dai sauransu.
Kamar yadda ilimi kuma ya ba da gagarumar gudummawa wajen daga martabar fahimtar dan'-Adam ga rayuwa, ci gabantar da hanyoyin kerekere da kuma tsara rayuwar al'umma. Ya taimaka wajen biyan bukatun dan'Adam da kuma samo sabbin hanyoyi magance matsalolin rayuwa.

Babu makawa, kirkiro wutan lantarki, man fetur, radiyo da talabijin, hanyoyi rubutu da buge-buge da kuma na safara da dai sauransu, sun bude wa dan'-Adam sabuwar fahimta ta rayuwa. Kuma sanannen abu ne cewa a duk lokacin da fahimta da masani-yarmu da rayuwa ta karu, fahimtarmu ga addini da ma'anar imani ma za ta karu. Don haka ilimi abu ne da yake kira zuwa ga imani kana kuma abokin zaman rayuwa.

Hankali da kwarewa: Hankali shi ne fitilar dan'Adam a rayuwarsa, don haka a duk lokacin da mutum ya yi amfani da hankali kamar yadda ya dace, to ba makawa zai kai shi ga alheri da kuma tsamar da shi daga halaka, bata da kuma nadama.
Dan'Adam ya kasance mai aikata abubuwa da daman gaske a rayuwarsa, don haka ya mallaki

kwarewa daban-daban a rayuwartasa. A saboda haka, ya za ma dole ya yi amfani da wannan kwarewa da ya samu wajen kyautata rayuwarsa, kamar yadda kuma yake wajibi ya yi amfani da kwarewar sauran mutane a dukkan bangarori na rayuwarsa shi kadai, da na aure, tattalin arziki, siyasa, wayewa da dai sauransu.
A saboda haka ne ma, Alkur'ani mai girma ya yi mana umurni da amfani da hankali da kuma kwarewar al'umman da suka wuce. Don kuwa kwarewar mutane da kuma abubuwan da suka faru a baya na tarihi, bugu da kari kan abubuwan da hankali mutum ya kirkiro na ilimi, hikima da dai sauransu, abubuwa ne da suke taimakawa, nesa ba kusa ba, wajen tabbatar da kyakkyawar rayuwa da kuma bube sabbin kofofin fahimtarta.

Don haka ne Alkur'ani mai girma yake shiryar da mu zuwa ga amfani da kwarewar al'ummomi da kuma daidaikun mutane bugu da kari kan tunani da kuma amfani da hankali. Allah Madaukakin Sarki Yana ce wa:

"Kuma Shi ne Wanda Ya shimfida kasa, kuma Ya sanya duwatsu da koguna a cikinta, kuma daga dukkan 'ya'yan itace Ya sanya ma'aura biyu cikinsu. Yana sanya dare ya rufe yini. Lalle ne a cikin wancan, hakika akwai ayoyi ga mutane wakanda suke yin tunani". (Surar Ra'ad, 13: 3)

"Kuma ba Mu aika ba a gabanninka face mazaje, Muna wahayi zuwa gare su, daga mutanen kauyuka. Shin fa, ba su yi tafiya a cikin kasa ba, domin su duba yadda karshen wadanda suka kasance daga gabanninsu ta zama? Kuma lalle ne gidan Lahira shi ne mafi alheri ga wadanda suka yi takawa, shin fa, ba ku hankalta? Har a lokacin da Manzanni suka yanke tsammani, kuma suka yi zaton cewa an jingina su ga karya, sai taimakonMu ya je musu, sa'an nan Mu tserar da wanda Muke so, kuma ba a mayar da azabarMu daga mutane masu laifi. Lalle ne, hakika, abin kula ya kasance a cikin kissoshinsu ga masu hankali. Bai kasance wani kirkiran labari ba, kuma amma shi gaskatawa ne ga abin da yake a gaba gare shi, da rarrabewar dukkan abubuwa, da shiriya da rahama ga mutane wadanda suka yi imani". (Surar Yusuf, 12: 109-111)
An ruwaito Imam Ali (a.s.) yayin da yake huduba ga dansa Imam Hasan (a.s.), yana shawartarsa da yin amfani da kwarewar sauran mutane, inda yake ce masa:

"don ka shirya wa karbar kwarewar wasunka ta hanyar tunaninka, don ka tsira daga fadawa cikin abubuwan da suka fada. Ta haka sai ka tsere wa wahalar nemansa da kuma wahalar gwaji. Don haka, sai ka ga ka san abin da muka gani kana muka shaida da ma abubuwan da suka

bayyana maka wadanda watakila mu ba mu riske su ba." Hakika a duk lokacin da muka samar wa kawukanmu ingantacciyar fahimta ta rayuwa, bisa ka'idojin shari'a, hankali da kuma ilimi, to za mu sami damar tafiyar da rayuwarmu cikin jin dadi da kuma nasara.
____________
1- Nahjul Balagah / hadawar Dr. Subhi Salihi / shafi na 393.