Dan'Adam Da Al'ummarsa

Fatima Muhammad Ahmad✍️
 Kaduna Press 

Al'umma, adadi ne na wasu mutane ko kuma zuriya wadanda suke da alakoki daban-daban a tsakanin junansu, kamar alaka ta akida ko kuma ta kusanci, ko kuma suna da manufa iri guda, ko kuma alaka ta tarihi da dai sauransu.

Kowane mutum yakan ji kusanci ko kuma jinginuwa ga zuriyarsa ko kuma al'ummar da ya fito daga cikinta, hakan kuwa don shi wani sashi ne na wannan zuriya ko kuma al'umma.

Mutum da al'ummarsa sukan yi musanyan amfanoni da suke samu a tsakaninsu. Haka nan ma ta hanyar al'umman da yake rayuwa a cikinta yakan iya tabbatar da hanyar rayuwarsa, dabi'u da kuma tunaninsa.

Lallai ba makawa dan'Adam yana da manufofi da yanayi masu cin gashin kansu, kamar yadda al'umma ma take da tata manufofi da yanayi masu cin gashin kansu. A lokuta da dama akan sami rashin jituwa tsakanin manufofin mutum da na al'ummarsa; don haka ne dokokin mutane da na Ubangiji suka ba da muhimmanci wajen tsara irin wadannan alakoki da kuma magance irin wadannan karo da juna da ake samu tsakanin manufofin guda biyu: na mutum da na al'umma. Koyarwar addinin Musulunci ya ba da muhim-mancin gaske wajen kyautata rayuwar mutum da ta al'umma; don kiyaye hakkokin wajibi na dan'-Adam, kamar yadda kuma ilmummukan kyawawan dabi'u da na zamantakewa suka ba da muhimmanci wajen gyara rayuwar mutum da ta al'umma, da kuma tabbatar da su bisa asasin kyawawan dabi'u da kuma 'yantaccen shu'uri.

Ko da yake wasu daga cikin mutane sun fi damuwa da tabbatar da manufofin kansu, ba tare da la'akari da manufofi da matsalolin sauran mutane ba.

Misali, dan kasuwan da ke boye abinci da kuma masu sanya kayayyaki su yi tsada, ba sa wani tunani in ban da yadda za su sami riba mai yawa. Ba sa tunanin irin halin da fakirai marasa abin hannu za su shiga saboda tsadar kayayyakin bukatun yau da kullum, su dai babban burinsu shi ne samun riba.

Haka nan mabukaci, ba ya tunanin kome face yadda zai biya wannan bukata ta sa ba tare da tunanin bukatun sauran mutane ba. A wasu lokuta, hakan kuwa yakan sabbaba wa mutane matsaloli masu yawan gaske.

Haka nan ma mutumin da yake da wata manufa ta siyasa, ba ya barci har sai ya cimma wannan manufa ta sa, ko kuma isa ga wani matsayi na siyasa da yake bukata. To amma idan har ya samu biyan wannan bukata, sai ka ga ba abin da ya dame shi na daga irin matsaloli da wahalhalun da sauran mutane za su shiga na rayuwa da kuma siyasa.

Haka kuma manomin da ya mallaki wata gona, ba ya hada kai da sauran manoma wajen samar da ruwan da za su yi amfani da shi a gonakin nasu matukar dai gonarsa ta samu ruwan.

Irin wadannan mutane ba sa dubin lamurra da kuma matsaloli face in suna da manufa da maslaha a cikinsu.

Manzon Allah (s.a.w.a.) ya yi bayani kan wannan matsala ta zamantakewa mai matukar muhimmanci, da kuma kan wannan son kai wanda yake matukar cutar da maslahohin al'umma. Inda yake ce wa:

 "Babu wanda zai yi imani daga cikinku (musulmai) har sai ya so wa dan'uwansa abin da yake so wa kansa na alheri ".

Ta haka ne Manzon Allah (s.a.w.a.) ya hada tsakanin tunani kan maslahohin al'umma da kuma fita daga son kai na mutum guda. Don mutum ma'abucin son kai wanda ba ya tunanin maslahohin al'umma, ba mumini ne na gaskiya ba. Kana kuma duk wanda ba ya tunanin maslahar sauran mutane, to babu wanda zai yi tunanin maslaharsa, to hakan

 1- Mizan al-Hikma na Muhammad Ri Shahri, juzu'i na 1 / (Hakikat al-Imam), shafi na 395.

kuwa zai kasance babbar kafar ungulu ga hadin kan al'umma da kuma ci gabanta. Matukar dai ingantaccen shu'urin taimakekke-niya bai tabbata ga mutum da al'umma ba, kana kuma matukar babu wasu dokokin da za su kiyaye maslahohin mutum da na al'umma. to ba makawa al'umma za su zamanto cikin rashin tsari da son zuciya, kana kuma da yawa daga cikin mutane za su kasance cikin wahalhalu. Daga nan kuma sai masu karfi su samu daman cutar da marasa karfi da kuma takura masu rayuwa.

Hakika shu'urin taimakekkeniya da kuma na kyawawan dabi'u da suke tare da mu, bugu da kari kan ka'idoji na Ubangiji madaukaka, suna kiranmu zuwa ga kiyaye maslahohin al'umma, kamar yadda kuma suke kiranmu zuwa ga kula da maslahohin da suka kebanta gare mu. Kuma a lokuta da dama maslahohin mutum guda sukan cutar da maslahohin al'umma, don haka ya zama wajibi mu nesance su.

A matsayin misali, lalatawa da kuma kara kudi a kan takardun kudi (rasidin kudi) yakan samar da makudan kudade ga masu wannan mummunan aiki, sai dai kuma hakan yakan haifar da mummunan gibi ga tattalin arzikin al'umma. To don haka ne ma dokokin Musulunci suka haramta wannan aiki da kuma hukumta masu yin sa.

To amma cikin ayyukan tsarkakakkun mutane muna iya ganin daidaituwa kan maslahar mutum shi kadai da kuma ta al'umma.

Daga cikin irin wadannan kyawawan ayyuka shi ne abin da aka ruwaito daga Shugaban musulmi, Abu Abdullah, Ja'afar bin Muhammad al-Sadik (a.s.). An ruwaito daya daga cikin sahabbansa (sunansa Mu'attab) wanda shi ne mai kula da harkokin cikin gidansa yana cewa: "Wata rana Abu Abdullah ya ce min, a lokacin kuwa farashin kayayyaki ya tashi a garin Madina,: ya ya yawan abincin da muke da shi?, sai na ce masa: muna da abin da zai ishe mu na tsawon watanni. Sai ya ce: Fitar da shi ka sayar wa mutane, sai na ce masa: babu abinci a garin Madina fa. Sai ya ce: ka sayar dai, to lokacin da na sayar, sai ya ce min: je ka dinga saya tare da mutane rana-rana.

Sai Imam Sadik ya ce: Ya Mu'attab, ka sanya abinci iyalaina ya zamanto rabi sha'iri rabin kuwa alkama, hakika Allah Ya san cewa ina da karfin ciyar da iyalaina da alkama, to amma ina son Allah Ya gan ni ina kyautata rayuwa gwargwadon bukatata"

Wannan kissa tana nuna mana irin yadda Musulunci yake ba da muhimmanci a aikace ga al'amurran da suka shafi al'umma.

Don Imam Sadik (a.s.) ya ki yarda ya ajiye abincin da zai ci na watanni ga iyalinsa, a daidai lokacin da sauran al'umma suke cikin rashi da kuma kuncin abin da za su ci na rana guda. Kana kuma ya aikata hakan ne don wanda yake da karfin sayan abinci da yawa ya tara a gidansa ya nesance
____________
 1- Al-Kafi na Kulaini / juzu'i na 5/ shafi na 166, Darul Kutub al-Islamiyya.

yin hakan don a samu kayayyakin abincin a kasuwa da yawa, ta yadda kudinsu za su sauko kasa kuma marasa karfi su sami daman saya. A nan za mu ga ce wa Imam Sadik (a.s.), kamar yadda ya ba da muhimmanci ga al'amarin al'umma, to haka ma a bangare guda ya bai wa lamarin kula da iyalansa nasa muhimmancin shi ma. To wannan shi ne cikakken imani na gaskiya.

A nan yana da kyau a fahimci cewa, abu mai wahalar gaske ga mutumin da ya cutar da al'umma shi ma ya tsira daga zafin wannan cutarwa, don kuwa a dabi'ance mutum yana so ya rayu cikin al'umma wacce take cikakkiya wacce ta tsira daga dukkan cutarwa. To don haka matukar dai al'umma ba su tsira daga cutarwa ba, shi ma ba zai tsira ba, don kuwa shi ma cikin wannan al'umma yake raye.

 Please 🙏Share It To Youth's🌹