Rundunan yan sandan jahar Adamawa ta samu nasaran cafke wasu mutane biyar cikinsu harda mace yar shekaru talatin da haihuwa bisa zargin su da yiwa wata mata yar shekaru 33 da haihuwa fyade.

Kakakin rundunar ‘yan sandan jihar Adamawa D S P Suleiman Yahaya Nguroje ne ya tabbtar da haka a wata sanarwa da aka rabawa manema labarai a yola.

” D S P Nguroje yace an samu nasaran cafke wa’inda ake zarginne biyo bayan bayanan sirri da aka samu cewa wasu sun yiwa wata mata fyade a Greio dake anguwar Jambutu a cikin karamar hukumar yola ta Arewa.
Wanda kuma hakan yasa Jami’an ‘yan sandan basuyi kasa a gwuiwa ba inda nan take suka halarci wurin kuma sukayi nasarae kama mutanen da ake zargin.

”DSP Suleiman yace yanzu suna cigaba da bincike kuma da zaran sun kammala bincike zasu gufanar dasu a gaban kotu domin su fuskaci shari’a.

Daga karshe kwamishinan ‘yan sandan jihar Adamawa ya gargadi Al’ummar jihar da su nisanta kansu daga irin wadannan bata gari tare kuma da kai rahoton duk wanda ya aikata laifi ga Jami’an tsaro domin daukan mataki .

Wadanda aka kama da zargin yin fyaden dai sun hada da Ahmad Ismail dan shekaru 20 da Salu Buba mai shekaru 25 da kuma Muhammad Ali shikuma shekarun sa 28 sai Abubakar Ali yanada shekaru 28 da kuma Zainab Jafaru yar shekaru 30 da haihuwa.