Filing Talla

Filing Talla Ga Mai Bukata Sai Ya Tuntube Mu

AN GUDANAR DA TARON KYAUTATA ALAKA TSAKANIN HARISAWA DA SAURAN JANIBOBIN HARKAR......


Ajiya laraba 24 ga watan 6 Shekarar 2020, Yan uwa Harisawa na Imam Bakir zone yankin Kaduna unit, sun gudanar ta taron kyautata Alaka Tsakanin Harisawa da janibobin Harkar Islamiyya, karkashin jagorancin Sheikh Ibrahim Zakzaky.
Taron dai ya samu halartan tsofin Harisawa da matasan harisawa, da sauran janibobin Harkar Islamiyya. Taron dai ya guda na ne a muhalin Fudiyya rimi.
Malam Aliyu Bakin Ruwa da Malam Saminu tare da Malam Auwal da Kuma Hashim Bature, suka gabatar da jawabai awajen wannan taron. Inda su ka ga gabatar da jawabai a kan Klak, Siyasayar Duniya, Hadafin Harkar Islamiyya, Dangataka tsakanin Harisawa da janibobin Harka.
in da a karshe Wakilan yan uwa na Da'irar Kaduna Malam Aliyu Tirmizi da ya gabatar da jawabin rufewa, tare da tunatar da yan uwa nauyin da ya rataya a kan su, mu samman a wannan yanayin da muka tsinci kan mu a ciki, da halin da jagoran mu Sheikh Ibrahim Zakzaky ya ke ciki. Ya kuma yi kira ga yan uwa harisawa da su mutunta aikin su da bashi muhimmanci yadda ya kamata, sannan ya kira ga sauran janibobin Harkar da su bawa harisawa hadin kai a yayin gudanar da Ayyukan su, Sannan ya Kara da cewa: Yan uwa su tsayu akan koyarwar Sheikh Zakzaky. 
Sannan a kayi addu'o'i na mu saman ga jagora, Malam Sani Sarkin Malamai ya rufe taron da Addu'a.

Post a Comment

0 Comments

Close Menu