Filing Talla

Filing Talla Ga Mai Bukata Sai Ya Tuntube Mu

An Yi Tir Da Matakan Takura Wa Limamin Masallacin Aqsa

Kwamitin da ke kula da harkokin masallacin Quds ya yi tir da matakin gwamnatin Isra’ila na takura wa babban limamamin masallacin Quds.

kwamitin da ke kula da harkokin masallacin Quds ya fitar da wani bayani da a cikinsa ya yi tir da Allawadai da matakin da gwamnatin Isra’ila ta dauka na takura wa babban limamamin masallacin Quds Sheikh Sabri Ikrama.

A cikin bayanin da kwamitin da ke kula da masallacin Quds ya fitar, ya bayyana kafa dokar hana babban limamamin masallacin Sheikh Sabri Ikrama shiga cikin masallacin da cewa yana a matsayin keta hurumin masallacin.

Bayanin ya ce wannan mataki yana da alaka ne da irin matsayar da shehin malamin ya dauka, kan kare martabar wannan masallaci da kuma kare hakkokin al’ummar Falastinu.

A ranar Alhamis da ta gabata ce dai gwamnatin Isra’ila ta fitar da wani bayani da ke cewa, ta kara tsawaita dokar da ta kafa, da ke haramta wa babban limamamin masallacin Quds shiga cikin masallacin har zuwa watanni hudu a nan gaba.

Post a Comment

0 Comments

Close Menu