Filing Talla

Filing Talla Ga Mai Bukata Sai Ya Tuntube Mu

Arewa Na Cikin Yaƙi: Zubar Da Jinin Ya Isa Haka – Matasan Arewa


Shugaban kungiyar cigaban matasan Arewacin i Alhaji Muhktar Muhammad, yayi kira da babbar murya ga shugaban kasa Buhari da ya gaggauta kawo ƙarshen kisan da ‘yan bindiga ke yi a yankin Arewacin Najeriya ba tare da bata lokaci ba.

Shugaban matasan yayi kiran ne a yayin wani taron manema labarai da kungiyar ta kira a Kaduna, domin nuna bakin cikinsu da alhinin su dangane da kisan da ‘yan bindiga ke yiwa jama’a, musamman a yankin jihohin Katsina Zamfara da Sokoto.

Mukhtar Muhammad wanda ya ke jawabi cikin hawaye yace, babu wani mahaluki da ke cikin tsaro a kasar nan musamman yankin Arewa, halin da ake ciki yanzu shine an dauko wata hanya ta tarwatsa Arewa, domin abin da ke faruwa a kauyuka alama ce babba dake nuna ‘yan bindigar sun yi karfin da zasu iya tunkarowa birane.

Shugaban matasan ya yi kira ga shugaban kasa da ya yi gaggawar sauke shugabannin tsaro saboda gazawar su a fili, ya maye gurbin su da wadanda suka cancanta, ko kuma kasar ta fuskanci gagarumar zanga-zanga wacce ba ta taba gani ba.

Post a Comment

0 Comments

Close Menu