Daga Barrista Nuraddeen Isma'eel

Ingantaccen rahoton da yake 'Dauke da fasa aure ana saura kwana 3 za'a sha biki acikin Garin Zariya.

Su masoyan Bayan sun kwashe shekaru 6 suna tare suna Gudanar da soyayyar su Cikin lumana, bayan sanya ranar auren su Keda wuya kenan! shi Wanda zai aure ta' din inda yayi balaguro ya tafi Neman kudi Wanda zai samu ya rufama kansa a asiri Dumin yin hidimar kayan lefe.

Tafiyar sa Keda wuya' sai yarinyar da aka samasu ranar ta fara yi masa wulakanci, ta dawo bata 'Daukar kiran sa, idan yayi mata 'message'  sa'ko ta wayar hannu' sai taga Dama zata 'dawo masa da amsa, ganin haka yayi umarni ga iyayen sa, da suje gidan su yarinyar domin a Sanar da iyayenta halin da ita yarinyar take ciki.

Zuwan iyayen sa Keda wuya, sai mahaifin yarinyar yake Cewa' da sanin shi, yarinyar take duk abinda take ma shi saurayin nata. Sai iyayen yaron sukace ko zaka iya zantamana dalilanka na Barin yarinka tana irin Wannan Abin Baka 'Dauka mataki ba?

Bayan hakane! Mahaifin yarinyar da bude bakin sa yake Cewa' yana tuhumar shi saurayin 'Diyar nasa da Manyan laifuka guda 4 ata dalilin haka ne sukaji yaron ya fitar masu a rai.

Tuhuma ta farko itace! 
Tunda aka sanya masu rana, baya bata kudin kashewa, kuma bai mata kayan 'shopping' na azumin daya Gudana ba kimanin watana 1 da kwanaki daya wuce, sannan kuma baiyi mata kayan sallah ba, bugu da 'kari mahaifiyar yarinyar ta bashi 'Dinki na 'yan 'kannin bwacce aka sanya masu ranar ta bada Naira 1,000 akai mashi saida ya Amsa kudin sirikin nashi.

A dalilin haka ne aka fasa Wannan aure, inda sukayi da shi ya basu sati 2 don azo su Amshi kudin sa.

Hakan yafaru ne a wani gida da'ake kira da gidan sandan Balu dake unguwar nufawa Zariya, inda nan ne gidan su yarinyar.