Bayan shafe wata da watanni makarantu suna kulle sakamakon annobar cutar corona, gwamnatin tarayya ta bayyana wasu sharruda guda shida da kowacce makaranta za ta bi kafun a bude makarantun.

A cewar gwamnatin, kowacce makaranta sai ta samar da waɗannan ababe.

1) Wajen wanke hannu
2) Na’urar gwajin dumamar jiki
3) Na’urar kashe kwayoyin cuta a kowacce mashigar makaranta da kuma manyan wurare kamar su, Babbar kofar shiga, dakin kwanan dalibai, dakunan karatu, ofis da sauransu.
4) Kowacce makaranta za ta yi feshin kashe kwayoyin cuta a harabarta.
5) Dole ne kowacce makaranta ta kula da tsafta matuka.
6) Tabbatar da tazara a dakunan karatu da ofisoshi.