Filing Talla

Filing Talla Ga Mai Bukata Sai Ya Tuntube Mu

FYADE: Kungiyar Mata ‘Yan Jaridu Sun Gudanar Da Zanga – Zanga


Masu Zanga zangar kenan a adamawa

Biyo bayan yawaitar samun matsalar fyade yasa kungiyar ‘yan jaridu mata reshen jihar Adamawa suka gudanar da zanga zangar lumana zuwa gidan gwamnati domin nuna takaicin su dangane da yadda ake samun yawaitar fyade a tsakankanin al’umma kamar yadda Wakilinmu Adamawa, Alhassan Aliyu ya shaida mana.

” Da take bayani a madadin gwamnatin jihar, kwamishiniyar harkokin mata a jihar ta Adamawa Mrs Lami Patrick bayan ta nuna farin cikinta dangane da matakin da suka dauka ta tabbatar musu da cewa gwamnati basa tayi da wasaba wajen hukunta duk wanda aka kama ya aikta fyade wanda acewarta yawan fyade da ake yiwa mata cin mituncine da kuma bata musu rayuwa.

” Don haka dolene gwamnati ta dauki duk matakin da suka dace domin magance matsalar baki daya.
Mrs Lami ”tace zata Isar da sakon su zuwa majalisar dokokin jihar domin ganin an samar da doka mai tsanani kan duk wanda aka samu da lafin yin fyade.

Ta kuma kirayi iyaye suma su taimaka wajen sanya ido kan yaran su musamman mata domin ganin an samu saukin lamarin, domin a cewarta wani lokaci ana samun sakacin iyaye na nuna halin ko inkula da yaran nasu.

”Itama a nata jawabin, shugabar kungiyar ‘yan jaridu mata (NAWOJ) ta jihar Adamawa, Hajiya Zainab Sa’id Abubakar tace ”sun shirya zanga zangar lumanan ne duba da yadda fyade ke neman zama ruwan dare a tsakankanin al’umma, don hakane suka ga ya dace su nuna rashin jin dadin su dangane da lamarin, wanda acewarta wannan koma bayane ga rayuwar mata.

” Da wannan ne hajiya Zainab ke kiran gwamnati dama dukkannin masu ruwa da tsaki da su hada kai wajen yakan wannan mamunan dabi’a. Tace a shirye suke su marawa gwamnati baya waje daukan dukkan matakai da suka dace domin kawo karshen matsalar baki daya.

” Daga karshe ta shawarci iyaye da cewa suma suna da muhimmiyar rawa da zasu iya takawa wajen takawa lamarin birki.
Baya ga zanga zanga lumana da kungiyar tayi.Kungiyar ta kai ziyara wa kwamishinan ‘yan sandan jahar ta Adamawa C P Olubenga Adeyanju domin neman hadin kan Jami’an ‘yan sandan, Hakazalika kungiyar ta ziyarci majalisar addinin musulunci reshen jihar Adamawa tare da kungiyar kiristoci CAN domin niman goyon bayan su wajen yakan wannan matsalar ta fyade.

A wani labarin makamancin wannnan da Wakilin Jaridar Muryar ‘Yanci, Adamu Shehu ya aiko mana daga Jihar Bauchi, Kungiyar yan’jarida mata, reshen jihar Bauchi sun gudanar da zanga zangar lumana saboda yawaitar samun matsalolin fyade da yazama ruwan dare a Najeriya

Shugaban kungiyar Afsa Bulak tace ya zama dole a dauki mataki mai tsananin akan masu fyade domin kawo karshen lamarin.

Ya kuke Kallon wannnan matsalar ta fyade kuma wani mataki ya kamata a dauka fa masu aikata fyade?

Post a Comment

0 Comments

Close Menu