Filing Talla

Filing Talla Ga Mai Bukata Sai Ya Tuntube Mu

Hare-Hare A Jihar Katsina

Kashe-Kashe A Katsina:
Gwamnatin Tarayya Tana Zargin Sarakuna Da Sa Hannu

-KADUNA PRESS
Wasu daga cikin Sarakuna suna taimakawa’yan ta’adda, Mai Taimakawa Shugaban kasa kan Harkar yada labarai, Garba Shehu ne yayi ikirarin hakan.
Afirarshi da Gidan Talabijin na Channel TV a wani shiri mai taken Sunrise Daily ayau Monday, Shehu Garba yace, Sarakunan Gargajiya na taimakawa ‘Yan bindiga su gudu lokacin da jami’an tsaro ke kai samame maboyarsu.

‘Yan bindiga dai sun kasance a satin nan suna ta kai hare-hare musamman a jihar Katsina, a yadda suka kashe Mutane kusan 100 lokacin hare-harensu.
Shehu yayi zargin cewa, akwai mutane dake amfana da kashe-kashen.
“Ba wai muna zargin wane bane, amma ya fito fili cewa, har agarin da aka haifa shugaban kasa, ansamu wasu sarakuna dasa hannunsu ake kashe mutanensu,” yafada hakan.

“A zamfara, sarakuna da hakimai, da yawansu ankoresu daga ofishinsu.
“A wasu lokutan, Sojin sama sai da suka kai jiragen sama Katsina, kuma suna nan”
“A farkon kashe-kashen Zamfara, lokacin bala’in yana kan ganiyarshi a yankin, sai aka gane cewa, dazaran jirgin yaki ya tashi daga katsina zuwa zamfara, kafin yakai wasu sunkira waya, ‘yan ta’addan sun gudu”
“A karshe, dole sai da aka tilasta mana taso jirgi daga waje mai nisa, kamar Kaduna da Kano don kai dauki Zamfara.”

Shehu ya nemi mutanen kasa damu hada hannu, mu taimaka wa Jami’an tsaro da bayanai akan ayyukan yan ta’adda akan lokaci.” Dukkan mu a matsayin ‘yan kasa muna da aikin dake kanmu, damu bayarda bayanan ayyukan ta’addanci ga Jami’an tsaro.”
-KNPRSCD 06.
-15/06/2020.

Post a Comment

0 Comments

Close Menu