Yau zamuyi magana ne a kan Ka’idar Rubutun Hausa

>==> Isiya Sy✍️
Kaduna Press

Kasantuwar yanzu kowa ya zama dan media kan shi, a na ta rubuce rubuce ba fasali, muka ga ya dace mu dan kawo wannan dan takaicen cen rubutun, Dan an fanar da masu sha'awar rubutun a kafafen sadarwa.

Aiki da ka’idojin rubutun Hausa yana taimakawa matuka wajen saukaka karatu, da gane abin da kai kanka kake cewa, da kuma fahimta daga shi wanda kake karanta wa.

Babbabn abu shi ne sanin yadda ake harhada bakake a tada kalma.

Hakan ya hada da sanin cewa idan ka hade kalmar da ya kamata ka raba za ta bayar da wata ma’ana daban da wadda kake so.

Misali, idan na rubuta “koyaushe” a matsayin kalma guda, ma’anarta na nufin kowane lokaci, amma in na rubuta “ko yaushe...”, na soma yin tambaya ke nan da, watakila, ke bukatar kammalawa ko amsawa.

Misali, “Ko yaushe Rabeel zai zo?”

Idan aka yi kuskuren rubuta wadda ba ita ba ce, to za a faro karatun ba daidai ba, sai daga baya a gane ashe ba haka ya kamata a dauko karatun ba.

Haka batun dangantaka ko mallaka. Idan ka ce “rigarta” kana nufin wadda ta mallaka ke nan, amma idan ka ce “rigar ta...” to mai sauraro zai jira ya ji abin da rigar ta yi.

Salon karanta su ma daban yake. Da yake ba kowa ne ya san ka’idar rubutun Hausa ba sosai, shi ya sanya rubutun wani da Hausa, wanda aka yi ba kan ka’ida ba, yakan yi ma wani wuyar karantawa.

Kaduna Press 
Online Media News🎙️