Filing Talla

Filing Talla Ga Mai Bukata Sai Ya Tuntube Mu

Katsina: Masu Zanga-zanga Sun Ƙona Hotunan Buhari Da MasariAkalla sama da matasan dari uku ne, suka fito domin bayyana bacin ransu kan matsalar tsaro da garin Yantumaki ke fuskanta na hare-haren yan bindiga, wanda har ya kai ga kashe hakimin Yantumaki Alhaji Abubakar Atiku Maidabino a satin da ya gabata.
Wani Mazaunin garin Yantumaki ya shaida mana ta waya cewa Abinda ya harzuka matasan shi ne duk da akwai jami’an tsaro na soji da na Hana fasa kwabri a garin. Jiya cikin daren wajen karfe daya na dare, Yan bindigar sun shigo garin suna ta harbe-harben har suka tafi da Alhaji Mansur Yusuf Maidabino da diyarsa Fatima Yusuf. Kuma ko shekaran jiya sun sace direban wata mota da wasu dake cikin motar.
Ya kara da cewa safiyar yau, sai matasan suka hada kansu, domin nuna bacin ransu, da nuna rashin Jin dadin su kan abinda ke faruwa. Inda Suka bi tituna suka Kona tayoyi. Sun kona a wajen gari wato (bye pass) da kuma wajen gada da Kuma wajen hanyar Kankara. Suna zargin sojojin na jin karar harbin bindigar, amma ba su kawo Mana dauki ba.
Har zuwa lokacin aiko da wannan rohoto, rundunar ‘yan Sanda ta jihar Katsina, ba ta ce uffan ba, duk da sakon da aka turawa, Kakakin rundunar na jihar Katsina,SP Gambo Isa.

Post a Comment

0 Comments

Close Menu