Filing Talla

Filing Talla Ga Mai Bukata Sai Ya Tuntube Mu

Katsina: ‘Yan Bindiga Sun Hallaka Mutane 35
A daren jiya Talata ne, ‘yan bindiga bisa babura sama da dari da hamsin, dauke da bindigogi suka shiga garin Kadisau da ke karamar hukumar Faskari, inda suka kashe mutum talatin da biyar har lahira, sun kuma jikkata Mutum ashirin da biyu wanda yanzu haka wasu na kwance a asibitin garin Funtua da Dandume.

Wani Mazaunin garin na Kadisau ya shaida manata waya cewa “maharan sun zo ne da yammacin jiya talata da Misalin karfe biyar, suka fara harbe-harben kan mai uwa-da-wabi a garin. Mutane su kai ta gudun neman tsira, sun kwashe sama da awa ukku suna cin karensu babu babbaka a garin ba tare da Jami’an tsaro sun kawo mana dauki ba, duk da kokarin da muka yi na sanar da su.

Ya kara da cewa zuwa yanzu mun samu gawarwakin mutum talatin da biyar a safiyar nan, kuma muna cigaba da nema wasu. Yanzu haka mutanen kauyukan da ke Makwabtan mu suna cigaba da shigowa domin taimaka Mana, wajen ginar kabarin wadanda suka riga mu gidan gaskiya da yan bindigar suka kashe a daren jiya.

Duk kokarin da muka yi domin jin ta bakin kakakin Rundunar Yansanda ta jihar Katsina, SP Gambo Isa, abun ya ci tura har zuwa aiko da wannan rohoto


Safuwan Sp harun
Kaduna press
KNPRSCD 08


Post a Comment

0 Comments

Close Menu