Gamayyar Kungiyoyin arewacin Najeriya sun yi tir gami da Allah wadai da abinda suka kira miyagun kalamai na ɓatanci da mai magana da yawun shugaban kasa Femi Adesina ya yi akan Dattijo Farfesa Ango Abdullahi da yankin Arewa baki ɗaya.

Bayanin haka na kunshe ne cikin wata takardar sanarwa da ta fito daga gamayyar ƙungiyoyin Matasan na Arewa wacce ta samu sanya hannun shugaban kungiyar na kasa Alhaji Yerima Shettima kuma aka rarraba ta ga manema labarai a Kaduna.

Matasan na Arewa sun ƙara da cewar ko kaɗan baza su lamunci duk wani cin mutunci da raini da wani zai yi ga Arewa ko dattawan yankin ba.

“Maganar da Farfesa Ango Abdullahi ya yi gaskiya ne na cewar Arewa ta samu mummunan koma baya a mulkin Buhari, kuma tabbas Arewa bata taɓa fuskantar zubar da jini a tarihin ta ba kamar lokacin Mulkin Buhari, saboda haka kalaman da Femi Adesina ya yi akwai rashin kunya da raina manya, wanda ko kaɗan ba zai faɗi irin wannan kalamai ga wani tsoho a yankin Yarbawa ba, muna kira da babbar murya da ya janye wadannan kalamai da ya yi sannan ya nemi gafarar al’ummar Arewa”.

Daga karshe matasan sun bukaci jama’ar Arewa da yin watsi gami da fatali da kalaman Femi Adesina, sannan su mike tsaye wajen gudanar da addu’a na ganin bayan Iftila’in da ke neman wargaza Arewa.