Daga Barrista Nuraddeen Isma'eel

Bayan wata budurwa mai kimanin shekaru 22 mai suna Maryam Nuraddeen a inda ta kulle kanta acikin 'Daki, ta dir'kama kanta allura mai 'Dauke da sinadarin guba.

Ita dai Wadannan budurwar tayi hakanne domin rabata da Wanda take s, take kuma 'Kauna, bayan kuma har ya turo magabatansa, a inda har aka Tsayar masu da ranar 'Daura auren su.

Amma duba ga yanda shi Wanda aka sanya masu ranar bashi da Abin hannu, ma'ana ba mai hannu da shuni bane'  ita kuma 'Diyar masu dashi ne, domin iyayenta suna da kudi. nan take sai ga babban mutum mai Mota, kuma mai kudi fiye dashi Wancan matashin da aka Tsayar masu da ranar auren, nan take iyayen watannan maryam sukayi alaragab da shi wannan mai kudin, suka Ce sun fasa baiwa shi Wancan 'Diyar su.

Nan akayi kira na iyayen shi Wancan Tsohon saurayin nata aka basu kudin su, Akace shi wannan daman basu aminta dashi ba, kawai yarinyace ta Dage shi take so, amma yanzu sun Canza Shawara, dun haka yaje ya Nemi wata a gaba.

Kazalika inda budurwar ta yanke Shawarar ta kashe kanta kawai, kowa ya rasa ta, da dai ace ta bijirema iyayen ta, domin ita Zuciyar ta bata aminta dashi mai kudin ba, bayan 'balle 'kofar ita budurwar da akayi inda aka ganta nan kwance tayiwa kanta allurar guba.

Amma nan take aka garzaya da ita asibiti Cikin gaggawa' inda a halin yanzu dai maryam bata mutu ba, amma ta'iya baiyana dalilin ta nayin hakan' sai iyayen ta suka sake Shawara suka kirawo shi Wancan Tsohon saurayin nata aka Mayar masu da ranar auran su, shi kuma mai kudi aka bashi ha'kuri.

Wannan Abin ya faru ne a Jahar kaduna, a 'karamar Hukumar soba.