Filing Talla

Filing Talla Ga Mai Bukata Sai Ya Tuntube Mu

Shugaba Buhari Yayi Bayani

SERAP:- Ya Kamata Buhari Ya Magantu.

-KADUNA PRESS.

SERAP ta bukaci shugaba Muhammadu Buhari da yabayyana cikakken sunayen wadanda aka kwato N800bn a wajen maha’inta.
A wata sanarwa da Mataimakin Shugaban Hukumar, kolawole oluwadare,ya fitar yana mai neman shugaban kasa da yabawa Ministan Sharia Abubakar Malami da Ministar Kudi Zainab Ahmed umarni dasu tabbatar sun bayyana kudin da aka kwato wajen wadanda sukai ha’inci.
Duba da dokar ‘yancin Neman Labari, SERAP ta bayyana cewa ” bayyana bayanai akan kudi N800bn da aka kwato wajen maha’inta, ya zama dole abi hanyoyi da suka dace wajen bayyana hakan.”

Kuma Hukumar takara neman Gwamnatin tarayya data bawa hukumar bincike da cin hanci dasuyi bincike sosai kuma afili akan Naira N51bn da aka sa cikin Asusun banki na mutane daban-daban a shekarar 2019.”
Acewar Oluwadare, “bayyana hakan, zai bayyana gaskiyar lamari asan ina kudin suke zuwa kuma meyasa suke cikin Asusun bankunan maban-banta, kuma zai bawa ‘yan kasa dama su san yadda za’ayi da kudinsu.”

Kadan daga cikin abinda aka rubuta cikin takardar da hukumar ta rubuta wa Ministan Sharia da Kudi ” Mutanen gari suna da ‘yancin su san yadda akayi da Naira N800bn da aka kwato gurin maha’inta, da kuma kudin da akace an baiwa dai-dai kun mutane acikin asusun ajiyarsu ta banki”
-KNPRSCD 06.
-14/06/2020.

Post a Comment

0 Comments

Close Menu