Filing Talla

Filing Talla Ga Mai Bukata Sai Ya Tuntube Mu

Lalacewar Tsaro: Mataki Zaka Ɗauka Ba Bada Haƙuri Ba – Sule Lamiɗo Ga Buhari


Tsohon gwamnan Jigawa Alhaji Sule Lamido ya caccaki Buhari a Twitter yayin da Jaridar Daily Trust ta wallafa wani labari.

Jaridar Daily Trust ta ruwaito shugaban kasa Muhammadu Buhari yana rokon ‘yan Najeriya da suke zanga-zanga da su kara hakuri kan batun halin tsaron da ake ciki musamman a Katsina da yankin Arewa Maso Yamma.

Sai dai a martanin da ya mayarwa da shugaban kasa Muhammadu Buhari a shafinsa na Twitter, tsohon Gwamnan jihar Jigawa, Sule Lamido ya gayawa shugaban kasa cewar, matasa da yawa sun mutu sabida murnar samun nasarar, Don haka babu dalilin da zai sanya ya roke su.

“Malamai da yawa sun yi huduba sun yi wa mutane barazana da shiga wuta idan ba su mara maka baya ba. Wasu ma sun sha kwata sun mutu sabida murnar samun nasararka”.

Daga Salisu Magaji Fandalla’fih

Post a Comment

0 Comments

Close Menu