Tun bayan aika-aikan da Sojojin Najeriya suka aikata a ranar 12 ga watan 12 Shekara ta 2015 a garin Zaria a kan Shaikh Zakzaky da almajiransa, gwamnati ke rike da shi ba tare da laifin komai ba. A yayin da almajiran Shaikh Zakzaky da dukkan masu son adalci suke ta kiraye-kiraye a sake shi, sai ga shi gwamnatin ta fake da cewa: wai tana tuhumar sa da sa mabiyansa kisan kai, alhali mabiyan nasa an yi shari'a da su a gaban kotuna daban-daban, amma sun kasa tabbatar da hakan, don haka kotunan suka sallami almajiran Shaikh din, kamar yadda shi ma babban kotun da ke Abuja ta yi umarni da a sake shi a shekarar 2016.

Mun samu rohotannin sirri a wannan makon da ya gabata cewa, akwai wani yunkuri da gwamnatin jihar Kaduna da jami'an tsaronta ke yi a kan almajiran Sheikh Zakzaky, musamman masu fita muzaharorin lumana na Free Zakzaky.

A wannan lokacin da hankalin duniya ya koma kan Annobar Coronavirus (COVID-19), jami'an tsaro suna so su yi amfani da wannan dama, wajen auka wa almajiran Sheikh Zakzaky na garin Kaduna da kama fitattun 'yan' uwa, musamman masu fita muzaharorin lumana na free Zakzaky da ake yi a duk mako.

Sannan sun dau hayar mutane daga wajen Kaduna, maza da mata, wasu za su kasance a cikin sahu, wasu a wajen sahu, a yayin da na ciki za su yi kokarin canza taken muzaharan, ko su tsokani jami'an tsaro a lokacin da suka zo wucewa. Sannan za su yi amfani da sandar shokin (shocking stick), wajen kama almajiran Sheikh Zakzaky, a yayin muzaharorin.

Don haka muna sanar da Al'umma, Harkar Musulunci karkashin Sheikh Ibrahim Zakzaky, ta barranta daga dukkan wani nau'i na tashin hankali kowane iri. Harkar Musulunci ba ta taba daukar matakin tashin hankali ba a tsawon shekaru sama da 40 na wanzuwar ta. Sanannen abu ne cewa Harkar Musulunci a Najeriya ba ta taba tayar da hankali ba, hatta a lokacin da ake tunzura ta. Wannan kam wani abu ne da ba zai canza ba duk tsananin tunzurawa.

Don Haka a karshe muna kira ga 'yan' uwa da su kasance cikin tsari, sannan duk wanda ya san muzahara ya kawo shi, to ya shiga sahu.

Za mu ci gaba da bin duk hanyoyin da suka dace, na doka da kuma kundin tsarin mulkin kasa domin cimma manufar mu, na ganin an yi wa Sheikh Zakzaky adalci.

Sannan  gangaminmu na lokaci-lokaci, da muzaharori da kuma fafutika duk za su ci gaba a lokacin da ya dace, a kuma a inda ya dace, kamar yadda muka saba ba tare da gajiyawa ba, ko tsoron takura ba. Har wala yau za mu ci gaba da neman hakkinmu a kotunan gida da kuma na kasa da kasa, kamar yadda muka yi a shekarun da suka gabata.

Daga karshe, za muyi amfani da wannan dama wajen kiran ’yan kasa na gari da su matsa wa gwamnatin Najeriya lamba ta mutunta dokar kotun kasa wajen sakin Jagoran Harkar Musulunci a Najeriya Shaikh Zakzaky ba tare da wani sharadi ba.

SA HANNU:
HURRAS KADUNA UNIT BANGAREN YADA LABARAI KARKASHIN HARKAR MUSULUNCI SHIYYAR DA'IRAR KADUNA.
13/6/2020.